Isa ga babban shafi

Akasarin kasashen Musulmi na bikin Sallah karama

Yau ta ke Sallah karama ga al’ummar Musulmi, bayan da a akasarin kasashe aka sanar da ganin jinjirin watan Shawwal, abinda ya  kawo karshen azumin watan Ramadana mai alfarma na shekarar 1444, bayan hijirar Annabi Muhammad Sallallahu Alayhi wa Sallam daga Makkah zuwa Madinah.

Wani karamin yaro yayin ddaukar hoton bidiyon taron Musulmin da ke halartar Sallar Idi karama a Bucharest babban birnin kasar Romania. 21 ga Afrilu, 2023.
Wani karamin yaro yayin ddaukar hoton bidiyon taron Musulmin da ke halartar Sallar Idi karama a Bucharest babban birnin kasar Romania. 21 ga Afrilu, 2023. AP - Vadim Ghirda
Talla

Hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa, da Qatar, Jordan da Sudan sun sanar da fara Sallar Idi a yau Juma'a. Saudiya kuwa tun da yammacin ranar Alhamis ta fitar da sanarwar ganin watan na Shawwal.

Sai dai a wasu kasashen da ke da rinjayen mabiya mazhabar shi'a, mahukunta sun bayyana ranar Asabar a matsayin ranar Sallar bayan azumin watan Ramadana.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamene'i da kuma babban malamin Shi'a na kasar Iraqi Ayatollah Ali Sistani, dukkaninsu sun sanar da cewa ranar ta Asabar za a fara Sallar Idin karama a kasashensu.

A Lebanon malaman Sunna sun ce za a fara hutun Sallar Azumin a yau Juma'a, yayin da wasu shugabannin mabiya Shi'a suka sanar da fara Sallar idin a ranar Asabar.

Kasar Oman ma za ta gudanar da Sallar Idi karama ce a ranar Asabar, kamar yadda Indonesia kasa mafi yawan al'ummar Musulmi a duniya za ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.