Isa ga babban shafi

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana karshen annobar Covid-19

A jiya Juma’a ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an kawo karshen annobar Covid-19, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da wargaza tattalin arziki da sha’anin zamantakewar duniya, sama da shekaru 3 bayan da ta ayyana ta a matsayin annoba.

Tedros Adhanom Ghebreyesus,shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya.
Tedros Adhanom Ghebreyesus,shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya. AP - Martial Trezzini
Talla

 Shugaban hukumar Tedros  Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da haka a jiya Juma’a, inda ya yi gargadin cewa har yanzu cutar na  nan  a matsayin barazana.

Wannan mataki na hukumar Lafiyar na zuwa ne bayan da kwamitin kwararru mai zaman kansa da ta nada a game da wannan  cuta ta Covid ya ce  cutar ba a bukatar mayar da hankali sosai a kan cutar daga hukumar.

Sai dai a cewar Tedros, hatsarin cutar bai kau ba, inda ya yi kiyasin cewa ta kashe sama da mutane miliyan 20 a fadin duniya, kimanin ninki 3 na mutane kusan miliyan 7 da aka ce ta kashe a hukumanvce.

A ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2020 ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cutar Covid-19 a matsayin annoba, makwanni bayan da ta bulla a birnin Wuhan na kasar China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.