Isa ga babban shafi

Tsananin zafi ya haifar da asarar rayuka a sassan duniya

Matsanancin yanayi a cikin watan Yuli ya haifar da barna a Kudancin Turai, Arewacin Afirka da wasu sassa na duniya.

Yadda jami'ai ke kokarin kwashe mutane a kauyen Gennadi na kasar Girka.
Yadda jami'ai ke kokarin kwashe mutane a kauyen Gennadi na kasar Girka. AP - Petros Giannakouris
Talla

Akalla mutane 34 ne suka mutu a kasar Aljeriya sannan an kwashe dubbai a wasu sassa na Turai sakamakon tsananin zafin da ya bazu a yankuna da dama na tekun Bahar Rum da sauran yankuna.

Gobarar daji ta barke a cikin dazuzzukan yankin Kabylia da ke gabar tekun Bahar Rum, sakamakon iska da ke kadawa a lokacin zafi da ya kai ma'aunin Celsius 48.

A ranar Laraba, gidan talabijin na kasar Aljeriya ya ce kasar ta yi nasarar shawo kan gobarar dajin da ke ci gaba da tashi a dazuzzukan ta, wanda kuma ya tilastawa kwashe mazauna wasu 1,500 daga gidajensu.

Arewaci da gabacin Aljeriya na fama da gobarar dazuzzuka a duk lokacin rani, Bahar Rum na bana ya tsananta.

Hakazalika an samu mummunar gobara a 'yan kwanakin nan a makwabciyar kasar Tunisia, musamman yankin Tabarka da ke arewa maso yammacin kasar.

Sama da mutane 300 ne aka kwashe daga kauyen Melloula da ke gabar teku a cikin kwale-kwale da kuma kan kasa. Jami'an kashe gobara na ci gaba kokarin shawo kan wutar a yankuna uku a arewa maso yammacin Bizerte, Siliana da Beja.

Tsananin zafi a cikin watan Yuli da ya haifar da barna a duniya, inda yanayin zafi ya kafa tarihi a China, Amurka da Kudancin Turai, wanda ya haifar da gobarar daji, karancin ruwa da barkewar cututtuka masu alaka da zafi da asibitoci.

Gobarar daji a Kudancin Turai

A tsibirin Sicily na Italiya, an gano gawarwakin mutane biyu a ranar Talata a wani gida da gobarar daji ta kone wanda ya rufe filin jirgin saman Palermo na wani dan lokaci, a cewar rahotannin Italiya.

Jami'an yankin sun ce gobara 55 na ci gaba da tashi a Sicily, a daidai lokacin da yanayin zafi ya kai 40 a ma'aunin Celsius.

A arewa maso gabas a Puglia, an kwashe wasu 'yan yawon bude ido 2,000 daga otal uku a Vieste yayin da wutar ta kama.

A kasar Girka, gobarar da ta tashi a tsibirin Rhodes a makon da ya gabata abin da ya tilastawa hukumomi gudanar da aikin kwashe mutane mafi girma da aka taba yi a kasar, inda aka tilastawa mutane fiye da 20,000 barin gidaje da otal-otal.

Gobarar za ta yi barna ga masana'antar yawon bude ido da ke zama jigon tattalin arzikin Girka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.