Isa ga babban shafi

Masu zanga-zanga sun yi arangama da jami'an tsaro a Girka

'Yan sandan kasar Girka sun harba barkonon tsohuwa, yayin da masu zanga-zanga sama da 40,000 suka fantsama kan tituna suna caccakar gwamnati, tare da nuna bacin ransu kan mummunan hatsarin jirgin kasan da ya auku wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 57 a watan jiya.

Masu zanga-zanga kenan da suka fito a Athens, babban birnin kasar Girka.
Masu zanga-zanga kenan da suka fito a Athens, babban birnin kasar Girka. REUTERS - STOYAN NENOV
Talla

Hotunan da aka yi ta yadawa a kafofin talabijin, sun nuna yadda aka yi arangama a dandalin Syntagma kusa da majalisar dokoki da ke tsakiyar birnin Athens.

Hatsarin da ya faru a ranar 28 ga Fabrairu ya fallasa gazawar tsaro na tsawon shekaru ga harkokin sufurin jirgin kasa a Girka, kuma ya sanya babban matsin lamba kan gwamnatin masu ra'ayin mazan jiya gabanin zaben kasar da ke tafe.

Zanga-zangar ta ranar Alhamis ta kasance tare da yajin aiki na sa'o'i 24, abin da ya kasance abu mafi girma da kungiyoyin kwadago suka kira, inda ya shafi ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kan su.

Yawancin masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin Firaminista Kyriakos Mitsotakis da ta yi murabus saboda hatsarin jirgin kasa mafi muni da ya afku a kasar.

An tuhumi shugaban hukumar da ke lura da harkokin sufurin jiirgin kasan da wasu jami’ai uku, amma fushin jama’a ya mayar da hankali ne kan rashin gudanar da ayyukan bunkasa hanyoyin layin dogon da aka dade ana tafkawa a kasar.

A makon da ya gabata, mutane 65,000 ne suka halarci zanga-zangar a fadin kasar, ciki har da kusan 40,000 a birnin Athens.

Baya ga mutane 57 da suka mutu, akwai wasu da dama da ke kwance a asibiti, ciki har da wani fasinja da ke cikin mummunan yanayi.

Ministan sufuri na Girka ya yi murabus bayan hadarin kuma Mitsotakis ya nemi kwantar da hankulan jama'a ta hanyar ba da hakuri tare da shan alwashin gudanar da bincike na gaskiya.

Harkokin sufurin jirgin kasa sun tsaya cik a fadin kasar bayan hadarin, kodayake mukaddashin Ministan Sufuri Georgios Gerapetritis ya ce a wannan makon sannu a hankali za a ci gaba da aiyukan daga ranar 22 ga Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.