Isa ga babban shafi

Guguwar Haikui ta tilasta kwashe dubban mutane a wasu yankunan Taiwan

Dubban mutane aka kwashe a Taiwan gabanin mahaukaciyar guguwar Haikui, tare da soke jigilar daruruwan jirage da kasuwanci yayin da hukumomi suka shirya tunkarar irin guguwar ta farko da ta afkawa tsibirin kai tsaye cikin shekaru hudu.

Mutane dauke da lema kenan, lokacin da guguwar Soudelor ta aukawa Hangzhou da ke lardin Zhejiang na kasar Taiwan ranar 7 ga Agusta, 2015
Mutane dauke da lema kenan, lokacin da guguwar Soudelor ta aukawa Hangzhou da ke lardin Zhejiang na kasar Taiwan ranar 7 ga Agusta, 2015 REUTERS/Stringer
Talla

Guguwar mai gudun tsawon kilomita 140 a cikin sa'a guda, ta haifar da rufe makarantu da harkokin kasuwanci a yankunan kudanci da gabashin tsibirin a ranar Lahadi.

Hukumomi sun ce sun kwashe sama da mutane 2,800 a cikin garuruwa bakwai, akasarinsu daga lardin Hualien mai tsaunuka, dake makwabtaka da Taitung.

Sojoji dauke da kayan aiki, kamar motoci masu sulke da kwale-kwale na roba, sun bazama a kusa da sassan Taiwan inda ake sa ran Haikui za ta fi yin tasiri.

Guguwa ta karshe da ta afkawa Taiwan ita ce Typhoon Bailu a shekarar 2019, wadda ta yi sanadin mutuwar mutum daya.

Ana sa ran Haikui ba za ta yi tsanani ba fiye da Saola, wadda ta ketare Taiwan amma ta haifar da mafi girman barazana a yankin Hong Kong da kudancin China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.