Isa ga babban shafi

Yawaitar bashi zai tilasta wa kananun kasashe zaftare kasafin kudinsu - Oxfam

Wani rahoton kungiyar Oxfam ya bayyana cewa matalautan kasashe za su zaftare kasafin kudinsu da kimanin dala biliyan 220 cikin shekaru 5 masu zuwa sakamakon tarin basukan da suka yi musu katutu.

Oxfam ya bukaci asusun bada lamuni na Duniya IMF da Bankin duniya kan su sassauta tsarin biyan bashin da kasashe masu tasowa ke fama da shi.
Oxfam ya bukaci asusun bada lamuni na Duniya IMF da Bankin duniya kan su sassauta tsarin biyan bashin da kasashe masu tasowa ke fama da shi. REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Kungiyar Oxfam da ke fitar da wannan rahoto yau Litinin dai dai lokacin da aka bude taron tattalin arziki a birnin Marrakech tsakanin asusun bada lamuni na duniya IMF da kuma bankin duniya ya bayyana cewa tarin basukan da ke kan kananan ko kuma matalautan kasashen ya sanya su biyan makuden kudaden ruwa wanda zai haddasa musu tarnaki wajen iya tafiyar da harkokinsu na kudi ciki har da kasafin shekara-shekara.

Rahoton na Oxfam, ya ce basukan kasashen wadanda za su ci gaba da biya zuwa nan da shekarar 2029 a jumlace suna biyan ruwa da uwar kudin da yawansa ya kusan kaiwa rabin dala biliyan guda a kowacce rana, wanda ke ci gaba da nakasa tattalin arzikinsu.    

Tarin kasashe masu tasowa ne yanzu haka ke fama da basuka akansu, dai dai lokacin da hukumomin kudi na duniya ke kara yawan kudin ruwan da suka sanyawa a kan kowanne bashi, a bangare guda ake fama da matsalar hauhawar farashi baya ga koma bayan tattalin arzikin da annobar Covid-19 ta haddasawa Duniya.

Rahoton na Oxfam, ya bukaci asusun bada lamuni na duniya da bankin duniya kan su amfani da yanayi da ake ciki na tarnaki tattalin arziki wajen saukaka tsare-tsaren biyan basukan maimakon tsaurarawa ga kasashen matalauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.