Isa ga babban shafi

Akalla mutane 40 ne suka makale a cikin wani rami a kasar India

Jami'an kai dauki a kasar India na iya kokari ganin sun ceto kusan mutane 40 da aka bayyana cewa sun makale a rugujewar wani ramin titin da ake ginawa a jihar Uttarakhand da ke arewacin India a yau  Lahadi.

Yankin Dharavi na kasar India
Yankin Dharavi na kasar India © John Wang / GettyImages
Talla

Rugujewar ta afku ne da sanyin safiyar yau Lahadi a jihar Himalayan ta Uttarakhand lokacin da gungun ma'aikata ke fita daga cikin rame.

An bayyana cewa kusan mita 200  na ramin sun ruguje.

Hanyar mota mai hada India da China
Hanyar mota mai hada India da China © 路透社图片

Dya daga cikin jami’an agaji na yankin mai suna Durgesh Rathodi, ya shaida wa kamfanin dillancin labaren Faransa  cewa "Kimanin ma'aikata 40 zuwa 41 ne suka makale a ciki. Ana isar da iskar oxygen ta cikin tarkace, amma karin tarkace na gangarowa yayin da masu aikin ceto ke kokarin kawar da wannan cikas."

Ana gina rami mai tsayin kilomita 4.5 tsakanin Silkyara da Dandalgaon don hada mafi kyawon wuraren ibadar Hindu na Uttarkashi da Yamnotri.

Rushewar gidaje a India
Rushewar gidaje a India EUTERS/Shailesh Andrade

Hotunan da jami'an ceto na gwamnati suka fitar sun nuna wasu tarin siminti da suka toshe ramen, tare da karkatattun sandunan karafa a rufin da ya karye a gaban baraguzan ginin.

Hatsari a manyan wuraren gine-ginen ababen more rayuwa sun zama ruwan dare a India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.