Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan tabarbarewar al'amura a Haiti

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar al'amura a Haiti da tashe-tashen hankula suka mamaye, yayin da Washington ke matsa lamba kan firaministan kasar Ariel Henry don ganin an sasanta rikicin siyasar kasar.

Wani jami'in tsaro Haiti a filin jiragen saman Port-au-Prince, 4/03/24
Wani jami'in tsaro Haiti a filin jiragen saman Port-au-Prince, 4/03/24 AP - Odelyn Joseph
Talla

Kasar Ecuado, wanda jakadanta a MDD José Javier De La Gasca Lopez-Domínguez ya kira taron na ranar Laraba, ta ce halin da kasar Haiti ke ciki na da matukar tada hankali.

Amurka ta yi kira ga firaministan Haiti Ariel Henry da ya gudanar da sahihin zabe, ba tare da kira da ya yi murabus ba – kamar yadda yake cikin muhimmiyar bukatar da shugaban kungiyar ‘yan dabar kasar Jimmy "Barbecue" ya gabatar.

Henry wanda ke karagar mulki tun bayan kisan shugaba Jovenel Moise a shekarar 2021, tun cikin watan Fabarairu ya kamata ya bar Mulki, amma ya dage da cewa  ya cimma yarjejeniyar raba madafun iko da 'yan adawa har sai an gudanar da sabon zabe.

Madugun ‘yan dabar ya yi gargadin a ranar talata cewa kasar zata hatgitse tare da haifar da yakin basasa muddun Henry ya ci gaba da rike madafun iko.

Kaddamar da hari

A makon da ya gabata wasu gungun ‘yan bindiga da ke rike da yankunan kasar sun kaddamar da wani yunkuri na hambarar da gwamnatin Henry, inda suka kai hari a tashar jirgin sama, gidajen yari da ofisoshin ‘yan sanda tare da yin barazanar kaddamar da yakin basasa.

Akalla mutane 15,000 ne suka tsere daga yankunan Port-au-Prince da rikicin ya fi kamari, kuma babban jami’in kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya ce lamarin ya wuce misali, inda aka kashe mutane 1,193 a fadin kasar cikin wannan shekara sakamakon rikicin ‘yan daba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.