Isa ga babban shafi

Haiti ta sanya dokar ta baci bayan tserewar fusrunoni dubu 4 daga gidan yari

Gwamnatin Haiti ta sanar da sanya dokar ta baci a sassan kasar a kokarin kwantar da hankula bayan tarzomar da ta biyo bayan balle gidajen yarin da ‘yan daba suka yi wanda ya kai ga tserewar fusrunoni fiye da dubu 4.

Tuni dai aka baiwa jami'an tsaro damar amfani da dukkanin karfi wajen dawo da fursunonin da suka tsere.
Tuni dai aka baiwa jami'an tsaro damar amfani da dukkanin karfi wajen dawo da fursunonin da suka tsere. REUTERS - Ralph Tedy Erol
Talla

A jiya Lahadi ne gungun ‘yan daban suka balle manyan gidajen yarin Haiti 2 wanda ya kai ga tserewar fursunoni akalla dubu 4 ciki har da gaggan batagari lamarin da ya tilastawa gwamnati sanya dokar ta bacin.

Gwamnatin kasar ta ce matakin sanya dokar ta bacin ta sa’o’i 72 wani yunkuri ne na bin sahun makasa ‘yan garkuwa da tarin batagarin da suka tsere daga gidajen yarin 2 mafi girma a Haiti.

Tuni dai aka baiwa jami’an ‘yansandan kasar amfani da dukkanin karfi don tabbatar da doka da oda, karkashin umarnin da mukaddashin Firaminista kuma ministan kudin kasar Patrick Boivert da ya basu.

Wannan lamari dai ya faru ne a dai dai lokacin da Firaminista Ariel Henry ke ziyara a kasashen ketare a kokarin samun goyon baya a kokarin sake girke dakarun kasashen duniya a kasar karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

Daga Alhamis din makon jiya zuwa yanzu, mutane 9 ‘yan daban na Haiti suka kashe ciki har da jami’an ‘yan sandan kasar 4 a hare-haren da suka ci gaba da kaiwa ofisoshin ‘yan sanda da tashar jirgin sama da babban filin wasan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.