Isa ga babban shafi

'Yan daba sun fasa babban gida yarin Haiti

Fursunoni da dama, wadanda ba a tantance adadinsu ba sun tsere daga gidan Yarin babban birnin kasar Haiti wato Porto-au-Prince, bayan mummunan harin da gungun mahara dauke da miyagun makamai suka kai, tare da fasa gidan Yarin a ranar Asabar da ta gabata.

Wasu 'yan Haiti yayin da dakarun tsaron kasar ke bincikensu.
Wasu 'yan Haiti yayin da dakarun tsaron kasar ke bincikensu. REUTERS - Ralph Tedy Erol
Talla

Kamar yadda aka yi fargaba dai, bayanai sun ce daga cikin fursunonin da suka tsere, akwai kasurguman ‘ya’yan miyagun kungiyoyin da suka dade suna tayar da hankulan ‘yan kasar ta Haiti, batun da jaridar Gazette Haiti da ake wallafawa a yanar gizo ta tabbatar.

Yayin da ita kuma Jaridar Le Nouvelliste ta ce cikin fursunonin da suka cika rigunansu da iska har da wadanda aka tsare tun shekarar 2021 a bisa zarginsu da hannu a kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasar ta Haiti  Jovenel Moise.

Jaridar ta kara da cewa majiyoyinta sun tabbatar da cewar tun ranar Alhamis din makon jiya maharan suka rika leken asiri kan gidan yarin na birnin Port-au-Prince ta hanyar amfani da jirage marasa matuka kafin farmakin da suka kai.

Jim kadan bayan fasa gidan Yarin ne kasurgumin dan daban da ya rikide zuwa dan ta’adda da ake kira da Barbecue ya ce  burinsu shi ne tilasta wa Fira Ministan Haiti Ariel Henry yin murabus.

Yanzu haka dai gungu-gungu na miyagun kungiyoyin da suka mallaki muggan makamai ne ke rike da ikon kashi 80 na daukacin babban birnin kasar Haiti Port-au-Prince, kamar yadda wani rahoton majalisar dinkin duniya ya tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.