Isa ga babban shafi

Firaministan Haiti ya kama hanyar murabus saboda matsin lambar 'yan daba

Firaministan Haiti Ariel Henry ya yada kwallon mangoro domin hutawa da kuda, wajen mika murabus dinsa a matsayin shugaban kasar da ke yankin Caribbean, bayan cimma matsaya da kungiyar kasashen yankin a matsayin mafita na warware rikicin siysar kasar.

Franministan Haiti, Ariel Henry, yayin ziyara a kasar Kenya. 1/03/2024
Franministan Haiti, Ariel Henry, yayin ziyara a kasar Kenya. 1/03/2024 AP - Andrew Kasuku
Talla

Shugaban kungiyar kasashen yankin Caribbean kuma shugaban kasar Guyana Irfaan Ali, wanda ya tabbatar da shirin murabus din Henry, ya yaba da matakin da ya kira wata dama ta kafa kwamitin shugaban kasa na rikon kwarya wanda zai nada firaministan rikon kwarya.

Henry mai shekaru 74 wanda ke rike da kujerar firanministan Haiti da ba zaben sa aka yi ba tun shekarar 2021, ya tafi kasar Kenya a karshen watan da ya gabata domin tabbatar da jagorancin tawagar tsaro ta kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya don taimakawa ‘yan sanda yaki da ‘yan fashi da makami, kafin dawowarsa gida ne rikicin neman murabus dinsa ya barke tare da mummunan tashin hankali a babban birnin kasar Port-au-Prince abin da ya tilasta masa makalewa a yankin Amurka na Puerto Rico.

Bukatar 'yan daba

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin yankin suka gana da safiyar Litinin a kasar Jamaica da ke kusa da kasar, domin tattaunawa kan tsarin mika mulki a siyasance, wanda Amurka ta bukaci a gaggauta, daidai lokacin da wasu kungiyoyi ‘yan daba ke kira ga Henry ya yi murabus.

Shugaban 'Yan dabar Haiti Jimmy Cherisier, wanda ke kira fga firanminista Henry da ya yi murabus.
Shugaban 'Yan dabar Haiti Jimmy Cherisier, wanda ke kira fga firanminista Henry da ya yi murabus. AP - Matias Delacroix

Jami'an yankin sun tsunduma cikin tattaunawar da ta kunshi 'yan jam'iyyun siyasa na Haiti, kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyin farar hula da kungiyoyin addinai da nufin kafa majalisar mika mulki da za ta share fagen gudanar da zabukan farko tun shekara ta 2016.

Henry, wanda da yawa daga cikin 'yan kasar Haiti ke kallon a matsayin mai cin hanci da rashawa, ya sha dage zaben yana mai cewa sai an fara maido da tsaro.

Amurka ta shiga tsakani

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya sanar da karin dala miliyan 100, domin ba da gudummawar aikewa da dakarun kasa da kasa zuwa kasar Haiti, bayan wata ganawa da ya yi da shugabannin yankin Caribbean a kasar Jamaica ranar Litinin.

Sakataren harkokin wajen Amurka  Anthony Blinken yayin ziyara a kasar Jamaica domin warware rikicin Haiti. 11/03/24
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken yayin ziyara a kasar Jamaica domin warware rikicin Haiti. 11/03/24 AFP - ANDREW CABALLERO-REYNOLDS

Blinken ya kuma ba da sanarwar wani Karin dala miliyan 33 na taimakon jin kai da kuma samar da wata shawara ta haɗin gwiwa da shugabannin Caribbean suka amince da su da "dukkan masu ruwa da tsaki na Haiti don hanzarta canjin siyasa" da ƙirƙirar "kwalejin shugaban kasa."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.