Wakilan kasashen Yamma na taro kan yadda za a ceto kasar Haiti
Wakilai daga manyan kasashen duniya za su gana a yau litinin a yankin Karebiya, domin tunkarar halin da ake ciki a kasar Haiti, yayin da tashe-tashen hankulan kungiyoyin ‘yan daba suka gurgunta babban birnin kasar da ke fama da talauci tare da tilastawa jami'an diflomasiyyar kasashen waje tserewa a karshen mako.
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin ‘yan daba, wadanda tuni suka karbe ikon mafi yawan yankunan Port-au-Prince da kuma hanyoyin da suka bi zuwa sauran sassan kasar, sun yi barna a cikin 'yan kwanakin nan, yayin da suke kokarin hambarar da Firaminista Ariel Henry a matsayin shugaban kasa mafi talauci a Yammacin Duniya.
Kawancen kasashen yankin Karebiya CARICOM, ya gayyaci jakadu daga kasashen Amurka, Faransa, Canada da kuma Majalisar Dinkin Duniya zuwa wani taro a kasar Jamaica domin tattauna tashe-tashen hankula da kuma za a ceto kasar ta Haiti.
A ranar Lahadin da ta gabata ne, mataimakin shugaban kasar Guyana, Bharrat Jagdeo, ya ce kasashen za su nemi samar da tsaro tare da cire shakku ga al'ummar Haiti.
Yayin da lamura ke kara tabarbarewa, an gano yadda gawarwaki ke kwance a titunan Port-au-Prince inda hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta ce wannan tashin hankalin ya raba al’ummar Haiti 362,000 da muhallansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu