Isa ga babban shafi

'Yan majalisar Faransa sun amincewa kasar ta kulla yarjejeniyar tsaro da Ukraine

'Yan majalisar Faransa sun goyi bayan kulla wata yarjejeniyar tsaro da Ukraine, bayan tafka muhawara da ta raba kan 'yan majalisar game da sabbin tsare-tsaren shugaba Macron kan Ukraine din.

Wannan sabuwar yarjejeniya dai ta raba kan 'yan majalisar
Wannan sabuwar yarjejeniya dai ta raba kan 'yan majalisar AP - Thomas Padilla
Talla

Yarjejeniyar ta shekaru 10 ta kunshi yadda Faransa zata rika taimakawa Ukraine din da makamai, baiwa sojojinta horo da kuma bata kudade da yawan su ya kai Yuro biliyan 3.2.

Yaejejeniyar ta kuma kunshi kara tsaurara alaka da Rasha, to amma akwai wani abu mai kama da fitar da sojojin sauran kasashen turai daga Ukraine duk da dai ba’a fito karara an yi wannan bayanin ba.

Sai dai kuma wasu na ganin wannan yarjejeniya ka iya sake janyowa Shugaba Macron bakin jini a gurin ‘yan kasar da dama da suke fushi da shi saboda dalilai da dama.

Bayan kwashe tsahon lokaci ana tafka muhawara a zauren majalisar, ‘yan majalisa 372 sun amince da kulla yarjejeniyar sai wasu guda 99 da suka yi fatali da ita, yayinda 101 suka ki cewa uffan a kuri’ar da aka kada.

Babu dai wani cikakken bayani game da abinda Faransar zata mora a yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.