Isa ga babban shafi
Najeriya

Akalla Mutane 150 sun mutu a kogi a yayin tserewa harin Boko Haram

A Jahar Yobe da ke tarayyar Najeriya, akalla mutane 150 ne suka hallaka a kogi, a lokacin da suke kokarin tserewa daga harin ‘yan Boko Haram a wani kauye da ke jihar ta Yobe.

Talla

Lamarin dai ya faru ne a wani kauye mai suna Kukuwa-Gari, kamar dai yadda wasu da suka tsira da rayukansu suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Al’ummar yankin arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da fuskantar munanan hare haren mayakan kungiyar Boko Haram.

Yanzu haka dai rundunar Sojin kasar ta sanar da kaddamar da hare hare ta sama akan mayakan na Boko Haram dake labe a dajin sambisa.

Tuni dai Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya bukaci sabbin Manyan hafsoshin tsaron Kasar da su kawo karshen ta’addancin Kungiyar nan da watanni uku masu zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.