Isa ga babban shafi
Najeriya

Kerry na Ziyarar a Najeriya

Yau Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai ziyarci birnin Sokoto dake Najeriya dan ganawa da malaman addini da kuma bayana taimakon kasar sa wajen yakin da ta’addanci.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry REUTERS/Evan Vucci/Pool
Talla

Jihar Sokoto dai ita ce Cibiyar Daular Usmaniya wadda ta jaddada addinin Islama a karkahsin shugabancin Sheikh Usman Dan Fodio.

Mista Kerry zai kuma tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari a kan matsalar tsaro, da ta tattalin arzikin, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Najeriya ta kwashe tsawon shekaru ta na fama da rikicin kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar da kuma na baya-baya nan da ta ke fuskanta na 'yan tada kayar baya a yankin Niger Delta mai arzikin mai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.