Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaman soji a yankin mu zagon kasa ne ga shirin zaman lafiya-inji Avengers

Kungiyar ‘yan tsagerun Niger Delta Avengers ta ce ci gaba da zaman sojoji a yankin na zagon kasa ga shirin zaman lafiyar da shugaban kasar ya kaddamar, kuma wannan ya sa suka ci gaba da kai hare-hare kan bututun mai a Yankin.

Tsagerun Niger Delta na ci gaba da fasa bututun mai a yankin Naija Delta.
Tsagerun Niger Delta na ci gaba da fasa bututun mai a yankin Naija Delta.
Talla

Sanarwar da kungiyar ta sanya a shafin ta na intanet, yace kada jama’a su zarge ta da ci gaba da hare-haren da ake samu, domin sun bayyana karara cewar suna bukatar ganin gwamnati ta janye daukacin sojojin dake yankin.

A ranar 1 ga watan nan ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da masu ruwa da tsaki daga Yankin Naija Delta inda suka gabatar masa da bukatu 16 cikin su har da janye sojoji daga Yankin.

Kungiyar Niger Delta Avengers ko NDA da ta bullo kwanan nan a yankin Niger Delta da ke da albarkatun man Fetur, ta ce burin ta shine samarwa yankin Mafita to kowacce hanya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.