Gwamnatin Najeriya na ganawa da Avengers
Shugaba Muhamamdu Buhari ya sanar cewar gwamnatin sa na tattaunawa da tsagerun Naija Delta dake ci gaba da fasa bututun mai da zummar shawo kan matsalar dake kokarin durkusar da tattalin arzikin Najeriya.
Wallafawa ranar:
Shugaban yace gwamnatin na nazarin shirin yin ahuwa ga tsagerun wajen basu kudi da koya musu aikin yi da kuma samar da tsaro a Yankin.
Sai dai a bangare daya kungiyar Naija Delta Avengers kamar yadda aka saba ta fitar da sanarwar cewar bata da labara wata tattaunawar da ake.
Mai Magana da yawun kungiyar Birgediya Janar Mudoch Agbinibo yace idan zasu tattauna da gwamnati dole sai an samu wakilan kasashen duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu