An nada Cazeneuve a matsayin Firaministan Faransa
Gwamnatin Faransa ta ayyana ministan cikin gida, Bernard Cazeneuve a matsayin sabon Firaministan kasar bayan Manuel Valls ya yi murabus daga wannan mukamin a yau Talata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mr. Valls ya ajiye aikinsa ne tare da amincewar shugaba Francois Hollande bayan ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugabancin kasar mai zuwa a karkashin inuwar jam’iyyar gurguzu.
A cewar Valls, ba ya fatan Faransa ta fada a hannun masu ra’ayin rikau, kamar dai yadda hakan ya kusa faruwa a shekara ta 2002, saboda haka zai gudanar da yakin neman zabe tare da kara nuna rashin amincewa da dan takarar adawa da kuma manufofinsa.
"Wannan dan takara ne da ba shi da manufofi face irin wadanda aka aiwatar a shekarun 1980, wadanda kowa ya tabbatar ba abin da suka haifar wa kasa face koma-baya" in ji Manuel Valls.
Mr. Valls ya kara da cewa, babban aikinsa a yau shi ne, sake hada kan magoya bayan jam’iyyarsu ta Socialist mai mulkin Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu