Isa ga babban shafi
Najeriya - Nijar

Issofou ya karrama Buhari da lambar girmar Nijar mafi daraja

Shugaban Jamhuriyar Nijar mai barin gado Mahamadou Issofou ya kai ziyarar aiki a Najeriya inda ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari a fadar sa dake Abuja a yau Talata.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadou Issofou, yayin karrama takwaransa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da lambar yabo mafi daraja ta kasar Nijar.
Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadou Issofou, yayin karrama takwaransa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da lambar yabo mafi daraja ta kasar Nijar. © Presidency / Femi Adesina
Talla

Shugaba Issofou da zai sauka a karagar mulki a watan gobe, ya yabawa Najeriya kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma hadin kan da suke samu wajen aiki tare musamman yakar ‘yan ta’addan da suka addabe su.

Daga karshe shugaba Issofou ya karrama Buhari da lambar girmar Nijar mafi girma ta kasa saboda inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu.

A nashi martani shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjinawa shugaban na Nijar saboda rawar da ya taka wajen shugabancin na gari da kuma yaki da talauci a tsakanin al’umma.

Shugaban Nijar Muhamadou Issofou yayin rattaba hannu kan wata takarda, bayan ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja.
Shugaban Nijar Muhamadou Issofou yayin rattaba hannu kan wata takarda, bayan ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja. © Presidency / Femi Adesina

Buhari yace wannan ya sa duniya ta yabawa shugaba Issofou kan irin gudumawar da ya bayar wajen samarwa kasar sa cigaba ta hakika duk da matsalolin da ake fuskanta.

Daga bisani shugaban Nijar Issofou ya kaddamar da wata hanyar da aka sanya sunan sa a birnin Abuja, inda ya samu rakiyar Gwamnonin Sokoto da Kano da Katsina da Jigawa da Yobe da kuma Borno.

Yabawa da jagorancin shugaban Nijar da kuma kin sauya kundin tsarin mulki kamar yadda wasu shugabannin Afirka keyi ta shi lashe lambar girmar Gidauniyar Mo Ibrahim mai dauke da kyautar Dala miliyan 5.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.