Isa ga babban shafi
GASAR-OLYMPICS

Kuyi mana aikin gafara - Sunday Dare

Ministan wasannin Najeriya Sunday Dare ya nemi afuwar al’ummar kasar saboda rashin taka rawar gani a wasannin Olympics da aka kammala a birnin Tokyo da kasar ta yi.

Sunday Dare, Ministan wasanni
Sunday Dare, Ministan wasanni © Premium Times
Talla

Najeriya ta kammala wasannin ne da azurfa guda da Blessing Oborodudu ta lashe da kuma tagulla guda da Ese Brume ta samu abinda ya baiwa kasar zama a mataki na 74 a teburin gasar kuma hakan ya janyo suka sosai daga masu sha’awar wasanni.

Dare ya bayyana wasu batutuwa guda biyu da yace sun shafi rawar da kasar ta taka a Tokyo da suka hada da dakatar da Yan wasa guda 10 da kuma wanke kayan wasannin da wani ‘dan wasa ya tsaya yi, matakin da ya haifar da cece kuce a ciki da wajen Najeriya.

Ministan wasanni Sunday Dare da Yan wasa biyu tilo da suka cire Najeriya kitse a wuta a gasar Olympics
Ministan wasanni Sunday Dare da Yan wasa biyu tilo da suka cire Najeriya kitse a wuta a gasar Olympics © Premium Times

Dare yace sun yi iya bakin kokarin su wajen ganin an cire haramcin da aka yiwa ‘Yan wasan Najeriyar amma hakan bai yiwu ba saboda rashin lokaci.

Ministan yace a matsayin sa na jagoran wasannin gaba daya ya dauki alhakin abinda ya faru, saboda haka yana neman gafarar jama’ar Najeriya akai, yayin da yake kare irin rawar da ‘Yan wasan kasar suka taka wanda yace shine mafi kyau a cikin shekaru 13 da suka gabata.

Yan tseren Najeriya a gasar Olympics
Yan tseren Najeriya a gasar Olympics © Premium Times

Dare yace ya kafa kwamitin bincike domin bankado abinda ya faru da kuma bada shawarar yadda za’a kaucewa sake aukuwar haka.

Ministan yayi watsi da masu neman batawa Yan wasan da suka wakilci Najeriya suna, yayin da ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da goyan bayan da ya basu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.