Isa ga babban shafi
NAJERIYA-AFIRKA TA KUDU

Najeriya da Afirka ta Kudu sun rattaba hannu akan yarjeniyoyin ci gaba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa sun jagoranci taron hadin kan kasashen biyu karo na 10 duk da matsalar samun sabon nau’in cutar korona da ta fito daga kudancin Afirka.

Shugaba Emmerson Mnagagwa da Muhammadu Buhari da Cyril Ramaphosa a Afirka ta Kudu
Shugaba Emmerson Mnagagwa da Muhammadu Buhari da Cyril Ramaphosa a Afirka ta Kudu © Nigeria presidency
Talla

Mai Magana da yawun shugaba Femi Adeshina yace bayan taron da suka jagoranta da kuma sanya hannu akan yarjeniyoyi daban daban, shugabannin biyu sun yiwa manema labarai bayani akan batutuwan da suka amince da su.

Yayin ganawa da manema labaran, shugaba Buhari ya bayyana ziyarar Ramaphosa a matsayin wadda ta samu nasara, duk da fargabar da ake da ita dangane da sabon nau’in cutar korona da aka yiwa suna Omicron.

Buhari yace kasashen biyu sun sanya hannu akan yarjeniyoyi da dama da kuma farfado da wasu da aka dade da rattaba hannu akan su domin ganin jama’ar kasashen sun ci gajiyar su.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afirka da suka halarci bikin bajen kolin Afirka ta Kudu
Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afirka da suka halarci bikin bajen kolin Afirka ta Kudu © Nigeria presidency

Shugaban yace daga cikin yarjeniyoyin da aka rattabawa hannu akwai ci gaban matasa da mata da kuma bunkasa rayuwar yara kanana da tintibar siyasa.

Sauran sun hada da sabunta wasu yarjeniyoyin da aka kulla a baya da suka hada da hadin kan soji da bangaren samar da wutar lantarki da hakar ma’adinai da kuma man fetur da iskar gas.

Buhari yace sun kuma kaddamar da wani sabon shirin tattaunawar matasa wadda ta baiwa matasa da dama shiga taron ta hanyar bidiyo, inda yake cewa matakin zai kawar da shingen da ake da shi tsakanin matasan kasashen biyu.

Shugaban yace kaddamar da majalisar bada shawara ta ministocin masana’antu da zuba jari zai baiwa ‘yan kasuwa na kasashen biyu da suka fi habakar tattakin arziki a Afirka damar bunkasa harkokin su da kuma samar da ci gaba.

Wasu daga cikin mahalarta bikin
Wasu daga cikin mahalarta bikin © Nigeria presidency

Buhari yace sun fahimci cewar suna bukatar daukar karin matakai domin dada hada kan jama’ar kasashen biyu domin cin gajiyar yarjejeniyar kasuwancin bai daya da aka kaddamar ta kasashen Afirka.

A nashi jawabi, shugaba Cyril Ramaphosa ya jinjinawa shugabannin Najeriya da Cote d’Ivoire da Ghana da kuma Senegal saboda nuna bacin ran su da suka yi da yadda kasashen duniya suka kakabawa Afirka ta Kudu da makotan ta dokar haramta zirga zirga sakamakon gano sabon nau’in cutar korona da aka yiwa suna Omicron da masana kimiyar ta suka gano.

Ramaphosa ya bayyana matakan da kasashen yammacin duniya suka dauka a matsayin kama karya da nuna wariya da kuma rashin fahimtar tanade tanaden ilimin kimiya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency

Shugaban Afirka ta Kudun yace ta hanyar hadin kai ne kawai za’a magance matsalar wannan annobar da ta addabi duniya, yayin da yake cewa illar da matakin haramta zirga zirgar zata yiwa kasashen dake kudancin Afirka na da yawa.

Ramaphosa yayi amfani da damar wajen kira ga kasashen da suka kakabawa yankin kudancin Afirka takunkumin hana zirga zirgar da su sake tunani akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.