Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

An zalunce mu maimakon yabo kan gano sabon nau'in Korona - Afirka ta Kudu

Hukumomin Afrika ta kudu sun bayyana takaicinsu kan matakin dakatar da zirga-zirgar sufuri da kasar da wasu kasashe suka yi sakamakon bullar sabon nau’in cutar Korona mai suna Omicron.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa. REUTERS/Sumaya Hisham/File Photo
Talla

A cewar hukumomin na Afirka ta Kudu, gano sabon nau’in cutar ta Korona na nuna jajircewar jami’an kiwon lafiyar kasar, amma a maimakon a yaba musu sai aka dauke matakin kulle musu iyakoki.

Hukumar lafiya ta Duniya WHO dai ta bayyana matukar damuwa kan matakin da kasashen Duniya suka dauka na kule iyakokin su ga Afirka ta Kudu.

Kawo yanzu Biritaniya, Jamus da Italiya da kuma Jamhuriyar Czech suka tabbatar da bullar sabon nau’in cutar Koronar na Omicron a cikinsu, abinda ya sanya Amurka, da Canada da Australia shiga cikin jerin kasashen da suka dakatar da zirga-zirga tsakaninsu da Afirka ta Kudu a ranar Asabar, saboda gano sabon nau’in cutar Koronar na Omicron a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.