Isa ga babban shafi
COP28

'Yan Najeriya na korafin tawagar mutane dubu 1 da dari 4 da suka je taron COP28

Gwamnatin Najeriya ta ce wakilai dubu daya da dari 411 da suka halarci taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya COP28 da ke gudana a Dubai, ba dukkaninsu ne kasar ta dauki nauyinsu ba, domin akwai ‘yan kungiyoyin fararen hula da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, da ke taka muhimmiyar rawa a bangaren da suka halarci taron daga kasar.

Wasu daga cikin wakilan tawagar Najeriya da ke halartar taron yanayi na COP28 na Majalisar Dinkin Duniya Dubai.
Wasu daga cikin wakilan tawagar Najeriya da ke halartar taron yanayi na COP28 na Majalisar Dinkin Duniya Dubai. © Nigerian Presidency
Talla

Mai taimakawa shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu wajen hulda da kafafen yada labarai, Temitope Ajayi ne ya bayyana haka a cikin sanarwar martani da ya fitar a safiyar yau Lahadi.

“Kungiyoyin matasa da dama daga Najeriya musamman daga yankin Arewaci da Neja Delta wadanda suka fi fama da matsalar hamada da kuma ayyukan samar da iskar gas ne suke halartar taron. Shugaban kungiyar matasan kabilar Ijaw Jonathan Lokpobiri ne ke jagorantar tawagar ‘yan kabilar Ijaw sama da 15 da suka yi rajista daga Najeriya. Daga cikin wakilan Najeriya kuma akwai ‘yan jarida sama da 20 daga kafofin yada labarai daban-daban.”

Sai dai hadimin shugaban kasar bai bayyana yawan adadin wadanda gwamnatin Najeriya ta dauki nauyinsu don halartar taron ba, duk da cewar ana zargin kimanin mutane dari 6 ne gwamnatin ta dauki nauyinsu.

Da dama daga cikin ‘yan kasar na sukar yawan wakilan Najeriya a taron, wanda ya sanyata zama kasa ta uku a duniya wajen yawan wadanda suka halarci taron na COP28, duk kuwa da kalubalan tattalin arziki da miliyoyin ‘yan kasar ke fuskanta sabida tsare-tsaren gwamnati.

Taron na COP28 shine karo na 28 da ke gudana a Dubai, ya kuma samu halartar mutane dubu 97 daga kasashe sama da dari a fadin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.