Nigeria: Makarantu 723 a Najeriya na rufe a jihohi 9 sakamakon rashin tsaro-UNICEF
Asusun kula da kananan yara UNICEF na MDD ya bayyana cewa akalla makarantu 723 ne yanzu haka a rufe a jihohi 9 na Najeriya, a yayin da aka jibge ‘yan gudun hijira a wasu da dama daga cikin su, a sanadin rashin tsaro ko kuma matsalolin da suka da ambaliyar ruwa da suka haifar da cikas ga ayyukan karantarwa.
Wallafawa ranar:
Alkaluman Asusun na UNICEF sun nuna cewa jihohin da wannan iftila’i ya shafa sun hada da Adamawa da Benue da Borno da Imo da katsina da Kebbi da Sokoto da Yobe da kuma Zamfara.
Asusun ya kara da cewa matsalar tsaro itace babbar matsalar da tafi shafar harkokin karatun wadda ya kai ga rufe su har na tsawon lokaci.
Majalisar dinkin duniya dai ta bayyana cewa cikakken zaman lafiya baya samuwa indai babu ingantaccen tsaro a cikin al’uma, don haka ya zama wajibi a hada karfi da karfe wajen tabbatar da tsaron a fadin kasar don samun bunkasar ilimi.
Matsalar rashin tsaron ta kasance tamkar tsinkewar wata muhimmiyar jijiya ce wacce in babu ita to dukkanin lamura sun dagule, Wanda hakan ya sanya baya ga rashin samun damar bude makarantu matsalar ta haifar da durkushewar harkokin tattalin arziki a sassan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu