Yara mata sama da miliyan 7 ne aka dakile wa damar samun ilimi a Najeriya
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, wato UNICEF, ya ce yara mata miliyan 7 da dubu dari 6 ne aka dakile wa damar samun ilimi a Najeriya, kuma galibin su daga arewacin kasar su ke.
Wallafawa ranar:
Wakiliyar asusun a Najeriya, Ms Cristian Munduate ce ta sanar da haka a Kano, da ke arewacin kasar, a yayin bikin tunawa da ‘Ranar ‘Yaya Mata ta Duniya ta shekarar 2023’, wanda aka yi a fadar gwamnatin jihar.
Ta ce a yayin da nasaroroin da ‘yaya mata ke samu ke bada kwarin gwiwa, lamarin da ke tayar da hankali shi ne rashin bai wa miliyoyin ‘yaya mata damar samun ilimi, matsalar da aka fi samu a arewacin Najeriya.
Ta ce wani abin tashin hankali a nan shine yadda Najeriya ke da kaso 15 na adadin yaran da aka ba sa zuwa makaranta a fadin duniya, tana mai cewa wannan kalubale ne babba.
Ta kara da cewa yayin da jihar Kano ke a matsayi na biyu wajen yawan ‘yaya mata da ba sa makaranta a Najeriya, akwai bukatar jaddada mahimmanci ilimi a matsayin makamin da ba kawai yake yakar jahilci ba, har ma da wargaza kangin talauci.
Tun da farko a wata tattaunawa da dalibai mata suka yi, sun yi bayani a game da dimbim kalubalen da ke kasancewa karfen kafa wajen neman ilimin ‘yaya mata, da kuma bukatar damawa da mata a bangarori dabam-dabam na rayuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu