Isa ga babban shafi

Fiye da kashi 50 na yara mata a Najeriya ba sa zuwa makaranta- UNICEF

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa fiye da kashi 50 na yara Mata a Najeriya basa zuwa makaranta, lamarin da ya fi tsananta a yankin arewacin kasar mai fama da matsalolin tsaro.

Wasu daliban makaranta sanya da hijabi a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.
Wasu daliban makaranta sanya da hijabi a birnin Kano da ke arewacin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Da ya ke jawabi gaban taron inganta ilimi da makarantun Faransa a Najeriya suka shirya, Jutaro Sakamoto, shugaban sashen ilimi na UNICEF ya ce yanzu haka akwai akalla yara mata miliyan 7 da dubu 600 wadanda basa zuwa makaranta a sassan kasar.

A cewar jami’in na UNICEF, wannan adadi ya kunshi yara mata miliyan 3 da dubu 900 da ya kamata ace suna matakin firamare baya ga wasu miliyan 3 da 700 a matakin karamar Sakandire.

Sakamoto ya bayyana cewa kashi 48 na adadin yaran mata da basa zuwa makaranta na yankin arewa maso yammaci da arewa maso gabashin Najeriyar ne, yayinda matsalar nuna fifiko wajen karatun yara maza da takwarorinsu mata ke ci gaba da ta’azzara musamman a jihohin arewacin 15.

Cikin makalar da jami’in na UNICEF ya gabatar, ya bayyana cewa kashi 9 ne kadai na yara mata da suka fito daga gidajen talakawa ke iya karatu a makarantun sakandire.

Kafin yanzu dai, Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda ake ci gaba da samun yara mata da basa samun damar zuwa makarantu a sassan Najeriya, matsalar da ta ce ta na ci gaba da ta'azzara ne sakamakon tsananin talauci da al'umma ke fama da shi baya ga matsalolin tsaro da suka yiwa wasu jihohin Najeriya katutu sai kuma nuna fifiko wajen bai wa yara maza ilimi fiye da mata da iyaye ke ci gaba da yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.