Kaka ya lashe takobin kokuwar Nijar
Yahaya Kaka na Jihar Tawa ya yi nasarar lashe takobi a kokuwar gargajiya ta bana da aka kammala a jihar Tawa karo na 38, bayan ya kayar da Lawali Dan Tela na jihar Zinder a fafatawar karshe.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kaka da a yanzu ya zama sabon sarkin takobi, ya kayar da Dan Tela ne bayan mintina biyu da 'yan dakikoki da bude fage.
A karo na 10 kenan da jihar Tawa ke lashe takobi a tarihin kokuwar wadda a bana 'yan wasa 80 daga jihohi 8 na kasar suka kece raini.
Sabon sarkin na cikin sabbin 'yan wasan kokuwa da taurarinsu ke haskawa a wannan lokacin a Jamhuriyar Nijar, kuma jihar Tawa na alfahari da shi.
Daga cikin kyaututtukan da Yahya Kaka ya samu sun hada da miliyoyin kudi na CFA da kujerar makka da kuma filaye.
A tarihin kokuwar dai, jihar Maradi nada takubba 10, sai jihar Tawa da ita ma ta samu 10 a bana, yayin da Zinder ke da 8, in da kuma jihar Doso ke rike da 4, sai kuma Niamey da Agadez da kowacce daga cikinsu ke da takubba 3.
Baki daga kasashe makwabta da suka hada da Najeriya na cikin mahalarta wannan kokuwar mai daukan hankula a Jamhuriyar Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu