Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar na ci gaba da shirye-shiryen bikin ranar jamhuriya

A Jamhuriyar Nijar, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da shirye-shiryen bikin zagayowar Jamhuriyar wato 18 ga watan Disamba mai zuwa, bikin da a wannan karo za a yi a garin Tawa.

Ana shirn gudanar da bikin ranar jamhuriya a garin Tawa na Nijar a ranar 18 ga watan Disamba mai zuwa
Ana shirn gudanar da bikin ranar jamhuriya a garin Tawa na Nijar a ranar 18 ga watan Disamba mai zuwa Crédit: Wikimédia commons
Talla

An tsara gudanar da ayyuka da dama da suka hada da gina gidaje, kawata gidan mai martaba sarkin tawa, filayen wasanni, hanyoyin mota, da kuma filin sauka da tashin jiragen sama da ke birnin.

A zantawarsa da sashen hausa na rfi, Mai Martaba Sarkin Tawa Alhaji Mahammadu Musa Salihu Galabi, ya bayyana shirin a matsayin wanda mutanen Tawa ke marhabin da shi.

Sarkin ya kara da cewa, babu shakka mutanen Tawa za su bada goyon bayan dari bisa dari game da ayyukan na zamani da za su kawata birnin.

Bukukuwan ranar Jamhuriya wata dama ce da gwamnatin Nijar ke ware biliyoyin kudade na CFA don kawata birane a sassan kasar a kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.