Isa ga babban shafi
Nijar

Harin ta'addanci ya hallaka jami'an tsaron Nijar 12

Wani sabon harin ta'addanci ya hallaka jami'an tsaron Jamhuriyyar Nijar 12 akan iyakar kasar da Mali, yankin da ke fama da karancin tsaro. Tuni dai ministan harkokin wajen kasar Mohammed Bazoum ya tabbatar da faruwar lamarin.

Wani Jami'in tsaron Jamhuriyyar Nijar kenan ke bayar da tsaro ga 'yan gudun hijirar da suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin boko haram, a wani kauye da ke jihar Diffa, kudu maso gabashin kasar.
Wani Jami'in tsaron Jamhuriyyar Nijar kenan ke bayar da tsaro ga 'yan gudun hijirar da suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin boko haram, a wani kauye da ke jihar Diffa, kudu maso gabashin kasar. REUTERS/Luc Gnago
Talla

A cewar Mohammed Bazoum za su gudanar da bincike kan lamarin, yana mai cewa kawo yanzu sun kafa kwamitin da zai nazarci batun.

Harin dai na zuwa ne bayan wanda ya faru a farkon watan Oktoba da ya hallaka sojin Amurka 4 da kuma na Jamhuriyyar Nijar da dama.

Wasu ganau sun shaidawa manema labarai cewa, tun da farko mayakan ne suka shigo garin na Ayorou da ke Tillaberi mai nisan kilomita 200 daga arewa maso yammacin Niamey babban birnin kasar, haye kan ababen hawa kimanin biyar, daga bisani kuma bayan artabu tsakaninsu da jami'an tsaron aka ga motocin jami'an tsaron na fita da gawakin 'yan uwansu.

Dama dai yankin na fama da karancin tsaro lamarin da ya tilastawa gwamnatin kasar sanya dokar ta baci a wasu yankuna.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.