Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta fara aiki da sabon tsarin biyan haraji

A wannan Laraba ake fara amfani da wani sabon tsarin biyan kudaden haraji da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta samar don cike gibin kasafin kudinta na bana.

Sabon tsarin karbar kudaden haraji ya fara aiki a Nijar
Sabon tsarin karbar kudaden haraji ya fara aiki a Nijar ©ISSOUF SANOGO/AFP
Talla

A karkashin sabuwar dokar, za a rika cire wani kaso na kudi da zaran kammala wata hada-hada musamman a cibiyoyin hada-hadaar kudade da suka hada da bankuna.

Dokar ta ce, dole ne a caji mutun wannan harajin matukar ya aike da kudi zuwa wani asusun banki a Nijar.

Sani Rabiu, masanin tattalin arziki kuma shugaban Kamfanin BNIF Afuwa a Nijar ya ce, gwamnatin ta kwaikwayi wasu kasashen ketere ne da ke amfani da irin wannan tsarin don samun kudin shiga, amma ya ce, lallai talakawa ne za su fi kokawa saboda akan su abin zai fada.

11:00

Sabon tsarin karbar haraji daga Kamfanoni a Nijar

Tuni kungiyoyin fararen hula suka bayyana rahin amicewarsu da sabon tsarin da suke kallo tamkar wani yunkurin musguna wa talakawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.