Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar: An soma dakon sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa

Miliyoyin 'yan Nijar ne suka kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar da na 'yan majalisa a yau Lahadi.

Wata mata yayin kada kuri'arta a zaben Nijar
Wata mata yayin kada kuri'arta a zaben Nijar YouTube/AFP
Talla

'Yan takara 28 suka fafata a zaben shugabancin kasar, yayin da a gefe guda kimanin ‘yan takara dubu 5 ke neman shiga majalisar dokokin kasar mai kujeru 171.

Da misalin karfe 7 na yammacin yau Lahadi aka rufe rumfunan zabe domin baiwa jami'ai damar soma kidayar kuri'un da aka kada.

Wannan dai shi ne karo na farko da ake sa ran farar hula ya mikawa farar hula mulki a Jamhuriyar ta Nijar, tun bayan juyin mulkin shekarar 2010 karkashin jagorancin Janar Salihu Jibbo.

Alkaluman hukumar zaben kasar sun nuna sama da mutane miliyan 7 suka cancanci kada kuri’unsu a zaben na yau.

Daga cikin ‘yan takara 28 da za su fafata kan kujerar shugabancin ta Nijar akwai, dan takarar jam’iyyar adawa ta RDR canji Mahaman Usman da kuma Bazoum Muhd na jam’iyya mai mulki ta PNDS tarayya, kuma tsohon ministan cikin gida wanda shugaba mai barin gado Muhd Issifou ke marawa baya.

Zaben na Nijar na zuwa ne yayinda dakarun kasar ke cigaba da kokarin murkushe hare-haren ‘yan ta’adda akan iyakarta da Najeriya daga barin kudu maso gabashi, sai kuma iyakar ta da Mali dake yankin kudu maso yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.