Isa ga babban shafi
Nijar

Al’ummar Nijar sun yi zaben shugaban kasa zagaye na biyu

Yau al’ummar Jamhuriyar Nijar suka kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa zagaye na biyu inda aka fafata tsakanin tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane na Jam’iyyar RDR Canji da kuma tsohon ministan cikin gida Bazoum Muhammed na Jam’iyyar PNDS Tarayya.

Wasu 'yan Jamhuriyar Nijar a birnin Agadez yayin kada kuri'a a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu. 21/2/2021
Wasu 'yan Jamhuriyar Nijar a birnin Agadez yayin kada kuri'a a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu. 21/2/2021 RFI Hausa / Oumar Sani
Talla

Karawar ta yau ta biyo bayan nasarar da 'yan takarar biyu suka samu a zagayen farko da aka yi a watan Disambar bara inda Bazoum ya zo na farko da kashi 39.03, yayin da tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane ya zo na biyu da kashi 16.98.

Bazoum mai shekaru 61 tsohon ministan cikin gida kuma babban aboki ne na shugaba Mahamadou Issofou mai barin gado, kuma tare suka kafa Jam’iyyar PNDS Tarayya kana suka yi gwagwarmayar da ta kaita shugabancin kasa.

Bayan tsayar da shi takara ya fuskanci sukar cewa bad an kasa bane daga abokan adawa kafin kotu tayi watsi da zargin.

Shi kuwa Mahamane Ousmane mai shekaru 71 da ake yiwa lakabi da ‘Maradonan siyasar Nijar’ saboda kwarewar sa ya zama shugaban kasa a shekarar 1993 kafin sojoji su kifar da gwamnatin sa bayan shekaru 3 sakamakon rikicin cikin gida daga kawancen Jam’iyyar sa da ta shafi Firaminista Mahamadou Issofou abinda ya kaiga Issofou yayi murabus ya kuam kulla kawance da Hama Amadou.

Wannan ya sa Ousmane ya hada kai da tsohon shugaban kasa Mamadou Tandja wanda ya kaiga sun samu nasarar zaben shekarar 1999.

Yanzu dai haka sauran Jam’iyyun da suka shiga takara a zagaye na farko na zaben Nijar sun bayyana kawance da wadannan Yan takara biyu domin mara musu baya a zaben na yau wanda zai bayyana wanda zai maye gurbin shugaba Mahamadou Issoufou wanda ke kawo karshen wa’adin shekaru 10 na mulkin sa.

Wanda ya samu nasara a wannan zabe zai zama shugaban Jamhuriyar Nijar na 10 bayan Hamani Diori da Seyni Kountche da Ali Saibou da Mahamane Ousmane da Ibrahim Bare Mainassara da Dauda Malam Wanke da Mamadou Tandja da Salihou Djibo da kuma shugaba mai barin gado Mahamadou Issofou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.