Isa ga babban shafi

Kungiyar AU ta kori Nijar daga cikin mambobinta

Kungiyar Tarayyar Afrika AU ta kori Jamhuriyar Nijar daga cikin mambobinta, abin da ke zama wani hukunci na baya-bayan nan da aka yanke wa kasar ta yammacin Afrika bayan juyin mulkin da sojoji suka yia  watan jiya. 

Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta kori Nijar daga cikin mambobinta.
Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta kori Nijar daga cikin mambobinta. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Bayan taron kungiyar a wannan Talata a birnin Addis Ababa na Habasha, kungiyar ta ce daukar matakin ya zama wajibi la’akari da yadda sojojin na Nijar suka ki bada hadin kan da ya dace a game da tattaunawar diflomasiya don magance rikicin siyasar kasar. 

AU ta kuma gargadi dukkanin mambobinta da su guji aiwatar da duk wani mataki da zai halasta gwamnatin sojojin da suka kawar da shugaban farar hula Bazoum Muhammad.

Matakin na AU na zuwa ne bayan da tuni ECOWAS da wasu kungiyoyin kasashen ketare suka sanar da kakaba wa Nijar takunkumai wadanda tuni suka fara tasiri a kanta. 

Sai dai kuma masana na ganin cire Nijar daga cikin AU ba zai yi mata wani tasiri ba, la’akari da yadda kungiyar ke zama tamkar dai ‘yar amshin shatan kasashen yamma a wasu lokutan. 

Bayan wannan mataki, kungiyar ta AU ta kuma ce za ta bibiyi irin matakan da kungiyar ECOWAS ko CDEAO ta dauka kan Jamhuriyar Nijar don ganin ta inda ya kamata ta kara shiga da nufin kara matsa lamba ga sojojin na Nijar. 

Janar Abdourahamane Tiani kenan, shugaban mulkin sojin Nijar lokacin da yake sanar da aniyarsu ta zama kan karagar mulki har tsawon shekaru uku.
Janar Abdourahamane Tiani kenan, shugaban mulkin sojin Nijar lokacin da yake sanar da aniyarsu ta zama kan karagar mulki har tsawon shekaru uku. © AFP

Sojojin na Nijar sun bayyana cewa, suna san su shafe tsawon shekaru uku kan karagar mulki kafin mayar da iko ga farar hula, matakin da ECOWAS ta ce sam ba za ta lamunta ba.

Kawo yanzu ECOWAS ba ta sauya matsayarta ba kan yiwuwar daukar matakin soji kan Nijar domin tilasta wa sojojin mika wuya tare da mayar da mulki ga farar hula.

Har yanzu dai al'ummar Nijar da kuma jihohin arewacin Najeriya masu makwabtaka da kasar na cikin fargaba tun lokacin da ECOWAS ta ce sojojinta na cikin shirin ko-ta-kwana domin kaddamar da farmaki kowanne lokaci.

Juyin mulkin na Nijar a karashen watan Yuli, ya tayar da hankalin kasashen yammacin Turai da sauran takwarorin kasar da ke karkashin mulkin farar hula a Afirka, wadanda suke fargabar mulkin sojin na Nijar ka iya kara wa kungiyoyin ‘yan ta’adda kwarin giwar tsananta hare haren da suke kai wa a yankin Sahel.

Wani karin batu kuma da ya zafafa adawar da kasashen ke yi wa sojojin da suka yi juyin mulki shi ne fargabar hakan zai bai wa Rasha damar samun gindin-zama a kasar da kuma fadada tasirinta a yankin na Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.