Isa ga babban shafi

Amfani da karfin Soji kan Nijar zai zama kuskure mafi girma - Issoufou

Tsohon shugaban Jamhuriyyar Nijar Mahamadou Issoufou ya yi gargadin cewa shigar sojojin ketare kasar don tilasta dawo da mulkin farar hula zai zama kuskure mafi girma, yana mai kiran cewa tattaunawar fahimtar juna ce kadai mafita ga halin da ake ciki.

Tsohon shugaban Jamhuriyyar Nijar, Mahamadou Issoufou.
Tsohon shugaban Jamhuriyyar Nijar, Mahamadou Issoufou. © France 24
Talla

Mahamdamou Issoufou wanda wannan ne karon farko da ya ke tsoma baki kan halin da ake ciki a Nijar tun bayan juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yuli, ya ce za a tafka babban kuskure idan har kasashen ECOWAS suka amince da amfani da karfin Soji kan Nijar.

Tsohon shugaban da ya mulki Nijar daga shekarar 2011 zuwa 2021, ya bayyana cewa abin damuwa ne matuka halin da Nijar ta tsinci kan ta amma shiga tsakanin Sojojin ketare ba zai magance ko kuma mayar da kasar kan turbar demokradiyya ba.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter ya ce idan har masu shiga tsakani suka rungumi tsarin tattaunawa ko shakka babu za a kai ga samun mafita a halin da Nijar ke ciki.

A cewar tsohon shugaban na Nijar, shigar Sojin ketare don yaki a Nijar da nufin dawo da mulkin farar hula zai haddasa tarin matsaloli ba kadai ga Nijar ba, har ma da kasashen makwabta ya na mai cewa dole shugabancin ECOWAS ya kiyaye wajen kaucewa tafka kuskure.

Mahamadou Issoufou wanda shugaba Bazoum Mohamed ya gada, ya ce kai tsaye shiga tsakanin kasashen ketare zai haddasa matsalolin tsaron da babu wanda zai iya hasashen lokacin iya kawo karshensu.

Duk da cewa har zuwa yanzu kungiyar ECOWAS ba ta sanar da lokacin fara amfani da karfin na Soji kan Nijar ba, amma kaso da yawa daga cikin mambobinta sun goyi bayan daukar wannan mataki baya ga Faransa da ke matsayin uwar goyon kasar ta Jamhuriyyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.