Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Bikin nadin mukamai a masarautar Malumfashi
A cikin shirin Al'adun mu na gado,za ku ji ko a ina aka kwana dangane da nadin wasu fittatun mutane da galadiman Katsina kuma hakimin Malufashi Dr Sadiq Abdullahi Mahuta ya yi a garin Malufashi.Bikin dai ya samu halartar manyan baki daga Najeriya da wajen kasar kamar dai yada za ku ji a cikin wannan shiri tareda Bashir Ibrahim Idris.11/02/202010:23 -
Yadda Chamfi ko Tsafi ke tasiri a wasan kokowar gargajiya a Jamhuriyar Nijar
Shirin lafiya al'adun gargajiya a wannan makon ya tabo yadda tsafi ko kuma chamfi ke karawa damben gargajiya armashi.31/12/201919:39 -
Ayyukan da suka rataya a wuyan sarakunan gargajiyar Afrika
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Mahamman Salissou Hamissou ya sake lekawa ne gidajen masarautun gargajiya a nahiyar Afrika domin nazari kan ayyukan da suka rataya a wuyansu.17/12/201910:23 -
Kalubalen da ya dabaibaye rubutun adabin Hausa
Shirin al'adunmu na gado a wannan makon tare Mahamman Salissou Hamissou ya tabo kalubalen dake fuskantar rubutun adabin hausa dama yadda za a magance matsalar.10/12/201910:13 -
Bikin mika takobin jagora Alhaji Umaru Futiyu Tall a birnin Dakar
A ranar 17 ga watan Nuwambar wannan shekara ta 2019 ne, Firaminista Faransa Edouard Philippe ya mika wa shugaban Senegal Macky Sall takobin Sarki kuma shugaban addini Alhaji Umaru Futiyu Tall, wanda turawan mulkin mallakar Faransa suka kwace sannan suka yi awun gaba da shi a shekara ta 1893.An gudanar da wannan biki ne a birnin Dakar fadar gwmanatin Senegal tare da halartar manyan jami’an gwamnatocin kasashen biyu, ‘yan majalisar dokiki sannan kuma da halartar tawagar zuriyar Sheikh Alhaji Umaru Tall.Mahaman Salisu Hamisu a cikin shirin al'adun mu na gado ya duba mana yada aka gudanar da wannan biki na Dakar.03/12/201910:00 -
Makomar sana'ar magungunan gargajiya: Gado Ko Haye?
Shirin Al’adun Mu Na Gado a wannan makon, ya waiwayi bangaren magungunan gargajiya ne, musamman kan wani babban taro na kasa da masu wannan sana’ar suka gudanar a garin Bauchin Nigeria, domin duba makomar wannan sana’ar da a baya ake dangantawa da gadon iyaye da kakanni, amma kuma yanzu yawanci ake yiwa shigar burtu. A da dai magungunan gargajiya sai gidan wane da wane watau ko dai Wanzamai, Masunta, Mafarauta, ko kuma Unguwar-zoma.19/11/201910:06 -
Nazari kan yadda Siyasa ta zama al'adar Kanawa
Shirin Al'adunmu na gargajiya a wannan makon, yayi nazari ne kan yadda sha’nin siyasa ya zamo al’adar mutanen jihar Kano dake yankin arewacin Najeriya, wannan kuwa na zuwa ne sakamakon lura da yadda a duk lokacin zabe ko na bayan sa, babu banbanci, kullum fagen siyasar jihar a raye yake da mahawarori.30/10/201910:49 -
Ana gab samun karin yare guda kan 11 da Jamhuriyyar Nijar ke da su a hukumance
Dai dai lokacin da Jamhuriyyar Nijar ke da yaruka 11 a hukumance yanzu haka wata sabuwar kabila da ta kira kanta da Tasawak ta bukaci sanya yarenta a jerin yarukan da hukuma ta amince da su.08/10/201910:16 -
Mulkin Turawa ya yi tasiri kan al'adun Najeriya
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Salissou Hamissou da Ibrahim Malam Goje, ya yi nazari ne kan yadda al'ummar Najeriya ta yi watsi da wasu al'adunta bayan zuwan Turawan mulkin mallaka daga kasar Ingila. Wannan shirin na zuwa muku ne a daidai lokacin da Najeriya ke bikin cika shekaru 59 da samun 'yancin kai. Kuna iya latsa hoton labarin domin sauraren cikakken shirin.01/10/201910:29 -
Tattaunawa da Rogazo mawakin gargajiya a Jamhuriyyar Nijar kan fasaharsa ta waka cikin zance
Shirin al'adunmu na gado a wannan karon tare da Salissou Hamissou ya tattauna da fitacce kuma fasihin mawakin gargajiya a Jamhuriyyar Nijar Rogazo wanda ya baje irin fasahar da Allah ya basa a salonsa na wake cikin magana.17/09/201910:37 -
Dambarwar da ta biyo bayan nadin sabon sarkin kabilar Shuwa Arab a Lagos
Shirin al'adunmu na Gado tareda Salissou Hamissou a wannan karon ci gaba ne kan yadda bikin nadin sarkin kabilar shuwa Arab ya gudana a Lagos, dama dambarwar da ta biyo bayan nadin sarautar.27/08/201909:58 -
Bukin nadin sarkin Shuwa|Arab na jahar Lagos
Shirin al'adu na wannan mako tare da Mohaman Salissou Hamissou, ya yada zanzo ne jahar Lagos da ke Kudu maso Yamman tarayyar Najeriya, inda al'ummar yankin arewacin kasar da ke zaune a jahar suke ci gaba da martaba jagoranci irin na gargajiya, matakin da yakai ga shehun Bornon nadin sabon sarkin kabilar Shuwa Arab na garin Lagos.15/08/201910:19
Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.