Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Shudewar al'adar kaciyar maza a gargajiyance a tsakanin al'ummar Kanuri
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' wanda Mohammane Salissou Hamissou ya shirya ya gabatar, ya yi dubi ne a kan yadda al'adar yi wa yara maza kaciya ke shudewa a tsakanin al'ummar Kanuri da ke jihar Borno a Najeriya.08/06/202110:13 -
Allah ya isa ga wanda ya sake kira na Bakatsine- Sabon Bagobiri
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako tare da Muhammad Salissou Hamissou ya tattauna ne game da wani mutun da ya sauya sheka daga Bakatsine zuwa Bagobiri, inda har ya ce, bai yafe wa duk wanda ya sake kiran shi Bakatsine ba daga yau. Tuni mutumin mai suna Mati ya mika fuskarsa ga wanzami domin yi masa tsagun Gobirawa. Kuna alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.01/06/202110:27 -
Waiwaye kan rayuwar Bob Marley da ya cika shekaru 40 da mutuwa (2)
A cikin shirin 'Al'adunmu Na Gado' na wannan makon Mohammane Salissou Hamissou dora a kan waiwaye a kan rayuwar Bob Marley, wanda ya cika shekaru 40 da mutuwa.25/05/202110:12 -
Waiwaye kan rayuwar Bob Marley da ya cika shekaru 40 da mutuwa
Shirin na wannan mako yayi nazari ne kan gudunmawar da marigayi Bob Marley ya bayar a fannin kidan zamani na Reggae, da kuma sauran tarihin da ya bari.19/05/202110:43 -
Tasirin haramta tashe a jihar Kano
Shirin Al'adunmu na Gargadjiya a wannan makon ya tattauna kan matakin hukumomin tsaro a Jihar Kano na haramta tashe, shirin ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan dalilan da ya sanya daukar matakin da kuma tasirinsa.11/05/202110:34 -
Yadda gwamnatin Kano dake Najeriya ta haramta wasannin tashe saboda tsaro
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Mahaman Salissou Hamissou ya yi dubi ne danagne da haramta gudanar da wasan 'Tashe' a Jihar Kano dake arewacin Najeriya, sakamkon yadda hukumomin tsaron jihar suka danganta wasan na al'ada dake gudana cikin watan azumin watan Ramada da batagari da ke amfani da damar wajen gudanar da aika-aika.05/05/202110:34 -
Dabi'ar taimako a lokacin Ramadan na shirin zama tarihi a tsakanin Hausawa
Shirin al'adunmu na gado tare da Mahaman Salissou Hamissou ya yi duba kan koma bayan da ake samu a cikin al'ummar musulmi musamman a lokacin Ramadan ta yadda masu galihu ke gaza taimakawa marasa karfi.04/05/202110:16 -
Yadda taimako ya yi karanci ga marasa galihu a watan Ramadan
Shirin Al'adunmu na gado tare da Mahaman Salissou Hamissou ya tabo yadda mawadata suka yi watsi da al'adar taimakon marasa galihu da hausawa suka saba a cikin watan Ramadan.27/04/202110:00 -
Harshen Hausa ya samu karbuwa a kasar Burkina Faso
Shirin Al'adun gargajiya na wannan makon yayi tattaki zuwa kasar Burkina Faso inda yayi nazari kan makomar harshen Hausa a kasar da kuma irin karbuwar da ya samu.13/04/202110:06 -
Matan da suka kafa daulolin mulki a nahiyar Afrika 2
Shirin na al’adun mu na gado a wannan mako dori ne kan shirin da ya gabata a makon jiya, inda muka kawo muku kadan daga cikin matan da suka kafa daulolin mulki a nahiyar Afrika, musamman kasashen Nijar Da Najeriya, inda kukaji mu da farfesa Ado Muhamman shugaban jami’ar Jihar Tawa da kuma malam Ibrahim Aminu Dn Iya masanin tarihi daga jihar kano.30/03/202110:52 -
Masarautun mata da suka yi fice a kasar Hausa
A cikin shirin 'Al'adunmu Na Gado' na wannan mako, Mohammane Salissou Hamissou ya yi nazari a kan masarautu ko daulolin mata da suka yi fice a kasar Hausa. A cikin shirin, akwai ganawa da manyan malaman tarihi da suka lakanci tarihin kasar Hausa.23/03/202110:49 -
Al'adar yi wa juna takwara a tsakanin al'ummar Kanuri dake jihar Borno
A cikin shirin 'Al'adunmu Na gado' na wannan mako, Mohammane Salissou Hamissou ya yi nazari a kan al'adar yi wa juna takwara a tsakanin al'ummar Kanuri, mahimmancinta da kuma yadda ta ke karfafa dankon zumunci, da ma yadda al'adar ke kaucewa daga alkiblarta.16/03/202110:24 -
Matakin hukumomin Najeriya na sanya tatsuniyoyi a manhajar Ilimi 2/2
Shirin al'adu na wannan mako tare da Mahaman Salissou Hamissou ya dora kan na makon jiya game da yadda hukumomin Ilimi a Najeriya suka amince da shigar da Tatsuniyoyi cikin manhajar Ilimin kasar, dai dai lokacin da tatsuniyoyin ke kokarin gushewa tsakanin hausawa duk da kasancewar su wani bangare na al'adun Hausawa.09/03/202110:26 -
Tarihin fataucin larabawa a nahiyar Afrika musamman yankin hausawa kashi na 2
Shirin Al'adunmu na Gado a wannan makon tare da Mohamane Salissou Hamissou ya duba yadda Larabawa suka shafe tsawon lokaci suna fataucin bayi a kasar Hausa.03/03/202110:31 -
Tarihin fataucin larabawa a nahiyar Afrika musamman yankin hausawa
Shirin Al'adunmu na gado a wannan makon tare da Salissou Hamissou ya duba yadda Larabawa suka yi shafe tsawon lokaci suna fatauci a kasar Hausa.23/02/202110:51
Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.