Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Bikin ranar nuna al'adun kabilar Tubawa a sassan Duniya- 2
Shirin al'adunmu na gado da ke zuwar muku kowanne mako tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya dora ne kan bikin kabilar tubawa da ya zo muku a makon jiya, kabilun da ke da matukar tasiri a kasashen Najeriya da Nijar.28/09/202210:13 -
Tasirin Masarautar Birtaniya ga Masarautun nahiyar Afrika
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan tasirin Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ga masarautun nahiyar Afrika, la'akari da kasancewar masarautarta daddiya kuma abar koyi ga galibin masarautun Duniya ta fuskar rike al'adu da dabbaka su.13/09/202210:12 -
Yadda aka gudanar da bikin ranar Hausa cike kayatarwa fiye da shekarun baya
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya mayar da hankali kan yadda aka gudanar da bikin ranar Hausa ta Duniya wanda a wannan karon ya gudana a kusan dukkanin kasashen yammacin Afrika da na Sahel baya ga Hausawan da ke zaune a wajen nahiyar Afrika da suka gudanar da nasu bikin na musamman.30/08/202210:06 -
Yadda harshen hausa ke mamaye kananan yaruka a Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan yadda harshen Hausa ke hadiye kananan yaruka tare da mamayar manyan yaruka a Najeriya da sauran kasashen makwabta.23/08/202209:54 -
Tarihin al'adar Sallar Biannu a garin Agadez na Jamhuriyar Nijar
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba kan bikin Biannu a jihar Agadez ta Jamhuriyyar Nijar, bikin da ya juye zuwa Sallah mai dogon tarihi a yankin na abzinawa da kusan kowa ke mararin isowarsa.16/08/202210:26 -
Yadda ake fuskantar bacewar kayakin tarihi a Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali bacewar gidaje da sauran muhimman kayakin tarihi a sassan Najeriya duk da kiraye-kirayen da ake yiwa mahukunta don alkinta irin wadannan kayaki.09/08/202209:34 -
Yadda aka kulla yarjejeniyar kawo karshen zaman kayakin tarihin Benin a Faransa
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya yi duba kan ziyarar shugaban Faransa a kasashen yammacin Afrika 3 ciki har da Jamhuriyyar Benin inda yayin zantawar shugabannin biyu wato Patrice Talon na Benin da Emmanuel Macron na Faransa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen zaman kayakin tarihin kasar a Paris. A yi saurare Lafiya.02/08/202210:02 -
Tarihin Masarautar Maradin Katsina
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya yi nazari ne kan tarihin Masarautar Maradin Katsina da ke Jamhuriyr Nijar.26/07/202209:42 -
Yadda Kabilar Koma ke rayuwar gargajiya a Adamawa
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon ya yada zango ne a dutsen Koma da ke jihar Adamawar Najeriya, inda ya tarar da mutanen Kabilar Koma da ke gudanar da tsantsar rayuwar gargajiya irin wadda aka yi ta dubban shekaru da suka gabata.19/07/202210:30 -
'Yan Kabilar Berom sun yi bikin nuna al'adu a jihar Filato
Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Isa ya tattauna akan bikin al'adun da 'yan kabilar Berom suka gudanar a jihar Filato.12/07/202210:03 -
Ci gaban tarihi da takaddamar da ta dabaibaye Masarautar Lokassa a Benin
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya dora kan shirin makon jiya da ya mayar da hankali kan tarihin masarautar Hausawan Lukusa, karkashin jagorancin mai martaba sarkin Hausawa kuma sarkin musulmin yankin Alhaji Abdu Nuhu.05/07/202210:41 -
Bikin nadin Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Inda
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan bikin nadin wazirin masarautar Katsina Sanata Ibrahim Inda wanda mai martaba Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya nada a ranar 11 ga watan da muke ciki na Yuni. Ayi saurare Lafiya.28/06/202209:38 -
Tarihin Masarautar Lokossa da Hausawa ke shugabanci a jamhuriyar Benin
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa ya yada zango a yankin Lokossa na Jamhuriyar Benin, inda wata takadama ta kuno kai a unguwar zongo dangane da wata masarauta karkashin shugabancin Nuhu Abdou .21/06/202209:55 -
Rikicin Masarautar Gindiri dake Filato
Bayan kwashe shekaru 18 ana tafka shari'a a kan rikicin Masarautar Gindiri dake Jihar Filato a Najeriya dangane da nadin Sum Fyem, kotun kolin Najeriya a karshen ta yanke hukunci wanda ya sabawa umurnin da ta bayar a baya. A cikin wannan shrin Abdoulayye Issa yayi bitar rikicin da kuma matsayin da kotun ta dauka akai.14/06/202210:35 -
Sana'o'in gargajiya da aka yi watsi da su a kasar Hausa
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' ya duba sana'o'in gargajiya da muka gada kaka da kakanni a kasar Hausa, da kuma yadda aka yi watsi da su a wannan zamani. An fara ne da batun girke girken gargajiya.24/05/202210:34
Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.