Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Ala'adar taimaka wa juna a tsakanin Hausawa da sauran kabilu a Togo lokacin Ramadan
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' ya mayar da hankali ne a kan tanade-tanaden al'adun Bahaushe, wadanda akasarinsu suka rungumi addinin Musulunci a game da tamakekeniya a lokacin azumin watan Ramadan. Shirin ya leka kasar Togo, inda ya tattauna da Hausa da ke zaune a wannan kasa tare da wasu kabbilu a game da hakan.28/03/202310:19 -
Yadda wasan Tabastaka ke taka rawa a fannin zaman lafiya a Nijar
Shirin "Al'adunmu na Gado" a wannan makon ya yi duba ne akan yadda wasan gargajiya na Tabastaka ke ta ka rawa wajen abinda ya shafi zaman lafiya a yankunan Damagaram da kuma Zindar.Haka nan kuma, shirin ya duba yadda al'ummar Hausawa suka rungumi abincin al'adar al'ummar kasar Ghana.Shirin bai tsaya nan ba sai da ya leka tarayyar Najeriya, inda ya kawo yadda aka gudanar da bikin nadin sabon Sarkin Kwantagora a jahar Niger da ke tsakiyar kasar.07/03/202309:56 -
An yi bikin nadin sarautar Sarkin Dogarawa na garin Tahoua
Shirin Al'adunmu na gargajiya a wannan makon ya tattauna akan bikin nadin sarautar garin Dogarawa da ke jihar Tahoua a Jamhuriyar Nijar.21/02/202310:08 -
Tarihin masarautar Fulani a jihar Lagos ta Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gidan sarautar, Sarkin Fulani a jihar Lagos ta Najeriya, Alhaji Abubakar Muhammad Banbado. Ayi saurare Lafiya.14/02/202309:52 -
Nadin Sarautar madakin Kanem a jihar Pulato ta Najeriya
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa wanda a ke tabo mana batutuwa masu alaka da al'adun gargajiya ko bukukuwan al'adu ko masarautun gargajiya a kasar Hausa, a wannan mako ma shirin ya yi duba kan Sarautar Madakin Kanem a jihar Pulato ta Najeriya.07/02/202310:13 -
Tasirin bikin al'adu na tunawa da dokin iska dan Filinge
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya sake yin duba kan tasirin gasar tseren doki da ya samo asali daga bikin al'adun tunawa da dokin iska dan Filinge karo na 6, Ayi saurare Lafiya.31/01/202310:18 -
Nadin sabon Sarki a garin Mayahe a Maradi karon farko a shekaru 70
Shirin Al'adun mu na gado a wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi tattaki zuwa garin Maradi na Jamhuriyyar Nijar inda ya yi mana duba kan bikin nadin Isa Gado a matsayin sabon sarkin Mayahe, nadin da ke zuwa bayan mutuwa Mai martaba Sarki Gado Sabo da ya shafe shekaru 71 a karagar mulki. A yi saurare Lafiya.17/01/202310:20 -
Tattaunawa kan tarihin dokin iska dan Filinge
Shirin Al'adunmu na Gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne zuwa garin Filinge a jihar Tillaberi, inda ya tattauna masana tarihi kan dokin nan da aka yi wa wakar "Dokin Iska Dan Filinge"10/01/202310:24 -
Rayuwar mata a fadodin sarakuna
Shirinmu na wanna makon ya yi dubi ne da yadda raayuwar mata take a fadodin sarakuna musamman a yanunan Hausawa. Shirin ya yi la'akari da yadda al'adun suke daga masarauta zuwa masarauta.13/12/202210:09 -
Shiri na musamman a kan rasuwar mawakiyar Jamhuriyar Nijar Hamsou Garba
Wannan shirin ya mayar da hankali ne a kan rashi da aka yi na mawakiyar Jamhuriyar Nijar Hamsou Garba, wanda aka haifa a shekarar 1958 a Maradi. Hamsou Garba ta shigaa harkar waka da wasan kwaikwayo, inda ta yi matukar fice a ciki da wajen Nijar.06/12/2022 -
Yadda aka kafa Masarautar Hausawa a Benin
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya kai ziyara ne can fadar mai martaba Sarkin Machina da ke jihar Yobe ta Najeriya da kuma Masarautar Hausawa a garin Port-Novo na kasar Benin.29/11/202209:33 -
Taron bajekolin zane-zanen gargajiya na yammacin Afrika a Lagos
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan taron bajekolin fasahohin kere-kere da zane-zanen gargajiya na yammacin Afrika da ya gudana a birnin Lagos na kudu maso yammacin Najeriya wanda aka yiwa lakabi da Art X. Ayi saurare Lafiya.08/11/202210:02 -
Lalacewar tarbiyya a tsakanin matasan Hausawa saboda kwaikwayon al'adun ketare
Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan lalacewar tarbiyya a tsakanin al'umma matsalolin da ake dora alhakinsu kan kwaikwayon dabi'un ketare a kasashen Hausawa.01/11/202210:02 -
Yadda aka gudanar da bikin ranar Maulidi a Najeriya
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya tattauna akan bikin ranar Maulidi da ya gudana a sassan Najeriya.11/10/202210:11 -
Tarihin kafuwar Zabarmawa a Najeriya da kuma barazanar gushewarsu
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa ya mayar da hankali kan tasirin kabilar Zabarmawa a Najeriya, da kuma kokarin da ake na hana gushewarta a sassan kasar duk da cewa kabilar ta fi yawa a jamhuriyar Nijar.05/10/202210:22
Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.