Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Bikin nadin sarautar Dan Iyan yamma a Ibadan Alhaji Abubakar
A cikin shirin al'adunmu na gado, za ku ji yadda Garba Aliyu Zaria ya bibiyi nadin sarautar Dan Iyan Yamma Alhaji Abubakar a Ibadan, basaraken da ke matsayin dan asalin kasar Nijar na farko da zai rike mukamin.02/02/202110:07 -
Nadin sarautar sabon sarkin kabilar Azibinawan Ittisana a Tahoua
Shirin Al'adun gargajiya na wannan mako yayi tattaki ne zuwa garin Tambai dake jihar Tahoua inda aka yi bikin nadin sarautar sabon sarkin kabilar Azibinawan Ittisana.12/01/202109:31 -
Bukin Manomar kabilar Sayawa a Bauchin Najeriya
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Mohamman Salissou Hamissou ya yada zango ne a jihar Bauchin Nigeria,inda kabilar Sayawa dake karamar hukumar Tafawa Balewa,ta gudanar da bukin Lim Zar da ta saba gudanarwa duk karshen shekara domin dabbaka al'ada da harshen na Sayanci.05/01/202110:16 -
Dalilan da suka haifar da matsalar daba a kasar Hausa
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan lokaci ya tattauna da masana kan dalilan da suka haddasa matasalar daba ko dabanci a yankin kasar Hausa da kuma ko matsalar tana da alaka da al'ada.15/12/202010:02 -
Karramawa da kuma kadammar da gidauniyar Marigayi Dr Adamu Dan Marayan Jos don taimakawa Marayu
Shirin al'adunmu na Gado a wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali kan bikin al'adun da ya gudana a jihar Plateau ta Najeriya inda yayin bikin aka kaddamar da gidauniyar karrama fitaccen mawakin gargajiyan nan Dr Adamu Dan maraya Jos, gidauniyar da za ta rika taimakawa 'yan Marayu.01/12/202011:05 -
Bikin kalankuwar Makafi a masarautar Damagaram ta Jamhuriyyar Nijar karo na 346
Shirin Al'adunmu na gado tare da Mahaman Salissou Hamissou ya mayar da hankali kan bikin kalankuwar makafi a masarautar Damagaram, bikin da ke da dadadden tarihi wanda bisa al'ada ke guda a duk karshen damuna bayan zuwan amfanin gona gida.24/11/202010:11 -
Yadda aka yi bukukuwan Maulidi a bana
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Muhammad Salissou Hamissou ya yi dubi ne kan yadda aka gudanar da bukukuwan maulidin Annabi Muhammadu (S.A.W).17/11/202010:16 -
Bikin cika shekaru 10 a kan karagar mulki na sarkin Wase na 14
Shirin 'Al'adunmu na Gargajiya' na wannan mako tare da Bashir Ibrahim Idris ya ziyarci masarautar Wase a jihar Filato, Najeriya, inda aka gudanar da bikin cika shekaru 10 na Sarkin Wase na 14, Dokta Muhammadu Sabo Haruna.10/11/202010:27 -
Matsayin wakokin fadakarwa a kasashen Hausa
Shirin al'adunmu na gado tare da Mahaman Salissou Hamissou ya duba tasiri da kuma muhimmancin wakokin hausawa ga al'umma.03/11/202010:23 -
Nadin sabon sarkin Zazzau Nuhu Bammali na 2, (kashi na 2)
A cikin shirin 'Al'adunmu na Gado', Mohamman Salissou Hamissou ya kawo mana ci gaban shirin makon da ya wuce a kan nadin sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.27/10/202010:28 -
Shiri na musamman kan bikin nadin sarkin Zazzau Ambassada Ahmed Nuhu Bamalli
Shirin Lafiya Jari ce tare da Salissou Hamissou a wannan makon, kacokan ya mayar da hankali kan yadda bikin nadin sarautar Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya gudana a matsayin sarkin Zazzau na 19.13/10/202010:21 -
Yadda tsaffin al'adun Hausawa ke fuskantar barazanar bacewa
Shirin da Al'adunmu na Gado a wannan karon tare da Salissou Hamissou ya tabo yadda wasu al'adun malam Bahaushe ke barazanar bacewa saboda zamani, Ayi saurare Lafiya.06/10/202009:30 -
Al'adar tauri a kasar Hausa
A cikin shirin"Al'adunmu Na Gado" na wannan mako, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi dubi ne da al'adar tauri a kasar Hausa.29/09/202010:15 -
"Sarkin Zazzau na da zumunci da kyauta"
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi dubi ne game da rasuwar marigayi mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris wanda ya yi ban-kwana da duniya a karshen da ya gabata yana da shekaru 84.22/09/202010:01 -
Alakar al'adar bikin Bianou da Musulunci
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Muhammad Salissou Hamissou ya yi nazari ne kan alakar da ke tsakanin dadaddiyar al'adar bikin gargajiya na Bianou da addinin Musulunci da ake gudanarwa a garin Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar.15/09/202010:18
Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.