Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Hawan daushen maulidi a Damagaram
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' ya yi tattaki zuwa jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar, inda aka yi hawan daushe a bikin Maulidin Annabi Muhammad S.A.W.26/10/202110:01 -
Yadda gasar tseren dawaki ke gudana a jihar Tillaberi ta Jamhuriyar Nijar
Shirin al'adunmu na gado tare da Rukayya Abba Kabara a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda ake shirya bikin wasannin gargajiya na sukuwar dawaki na shekara-shekara da aka saba gudanarwa a garin Filinge na jihar Tilaberri.19/10/202110:01 -
Mai martaba Sarkin Zazzau ya cika shekara guda a karagar mulki
Shirin al'adunmu na gado tare da Garba Aliyu Zaria ya yi duba kan yadda Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ke cika shekara guda cur akan mulkin masarautar ta Zaria.12/10/202110:03 -
Bikin Sallar Lasar Gishiri a Agadez ta Nijar
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon tare da Rukayya Abba Kabara ya yada zango ne a Agadez ta Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da bikin Cure Salee ko kuma sallar lasar gishiri bayan dakatar da shi tsawon shekaru biyu a dalilin annobar Korona.21/09/202110:00 -
Yadda sana'ar wanzanci ke neman shudewa
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' tare da Rukayya Abba Kabara ya yi dubi ne da yadda al'adar wanzanci ke neman shudewa a kasar Hausa saboda bullar masu askin zamani.14/09/202110:05 -
Yadda 'yan damben gargajiya ke amfani da sihiri
Shirin Al'adunmu na Gargajiya na wannan makon tare da Rukayya Abba Kabara ya tattauna ne game da sihiri ko kuma siddabaru tsakanin 'yan damben gargajiya.07/09/202110:02 -
Yadda aka yi bikin ranar Hausa ta duniya
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon ya tattauna ne kan bikin da aka gudanar kan ranar Hausa ta duniya a kasashen Najeriya da Chadi.31/08/202110:00 -
Bikin bayar da Sandar girma ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Rukayya Abba Kabara a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda bayar da sandar girma ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.17/08/202110:05 -
Yadda bikin ranar Hausa ta duniya ya samo asali
Shirin Al'adunmu na Gado ya tattauna ne game da bikin ranar Hausa ta duniya wanda kasashen Afrika akalla 50 za su gudanar a cikin wannan wata na Agusta. A cikin shirin za ku ji yadda wannan rana ta samo asali.10/08/202111:00 -
Taron karrama marubuci dan Najeriya a ofishin jakadancin Faransa
Shirin 'A'adunmu Na Gado' a wannan makon ya kawo liyafar karrama wani dan Najeriya, marubuci, Abubakar Adam Ibrahim da ofishin jakadancin Faransa ya yi a birnin Abuja na Najeriya.03/08/202110:37 -
Cibiyar raya Al'adun Faransa da Najeriya ta bude dakin karatu a Abuja
Shirin Al'adunmu na gargajiya a wannan makon yayi tattaki zuwa birnin Abuja dake Najeriya inda cibiyar raya Al'adun Faransa da Najeriya ta bude dakin karatu domin inganta musayar Al'adu tsakanin kasashen biyu.13/07/202110:45 -
Tarihin Masarautar Hausa ta farko a Legas
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan lokaci zai yada zango ne a Masarautar Agege, wadda ta kasance Masarautar Hausawa ta farko a birnin Lagos da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya da ta shafe shekaru 168 zuwa 200 da kafuwa06/07/202110:46 -
Gasar rubutun gajeren labari na harshen Hausa
A cikin shirin 'Al'adunmu na Gado', Mohammane salissou Hamissou ya kawo mana yadda wasu masu kishin harshenn Hausa suka shirya bikin gasar rubuta gajeren labari a cikin harshen Hausa, inda wadanda suka yi nasara suka lashe kyautuka.29/06/202110:39 -
Ranar Makada Da Mawaka ta duniya a Abuja
Anyi taron mawaka da makada a garin Abuja Nigeria da zimmar farfado da al'adun gargajiyan jama'a wanda aka fara wasannin a 1982.A cikin shirin Al'adunmu na Gado Mahamane Salissou Hamissou ya hada mana shiri na musamman.23/06/202110:25
Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.