Isa ga babban shafi
EU-Faransa-Birtaniya

Cameron yace harajin kudade zai cutar da Turai

Fira Ministan Birtaniya, David Cameron, yace zai hau kujerar na-ki game da duk wani yunkuri na sanya haraji kan hada hadar kudade, wanda Faransa ke shirin gabatarwa, shirin da ke samun suka daga sauran kasashen Yankin.

David Cameron na Birtaniya yana ganawa da  Nicolas Sarkozy na Faransa
David Cameron na Birtaniya yana ganawa da Nicolas Sarkozy na Faransa REUTERS
Talla

Cameron yace, idan Faransa tana bukatar sanyawa ‘Yan kasarta, to babu laifi, amma su ba zasu lamince a sanyawa sauran kasashen Turai ba.

Birtaniya tana fargabar idan har aka cim ma kirkiro da harajin tsakanin kasashe 27 na kungiyar Tarayyar Turai, bankunan da ke aiki a kasar zasu bar kasar zuwa kasashen Switzerland ko China.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yace ba zai jira sauran kasashen Turai ba domin amincewa da sabon kudirin harajin.

Sai dai kungiyar hada hadar kudade a kasar ta fito ta nuna adawa da shirin shugaban inda ta yi gargadin cewa matakin zai cutar da kasar Faransa idan sauran kasashen yankin Turai basu kaddamar da harajin ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.