Isa ga babban shafi
EU-Faransa-Jamus

Sarkozy da Merkel sun ce ci gaban Turai ne zasu ba muhimmaci

Bayan ganawarsu a birnin Berlin, shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun ce bunkasa ci gaban kasashen Turai shi ne zasu ba muhimmaci tare da bukatar kasar Girka sake salo kafin tallafa mata da kudaden da zasu farfado da darajar tattalin arikinta. 

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da Shugabar gwamnatin Jamus Chancellor Angela Merkel
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da Shugabar gwamnatin Jamus Chancellor Angela Merkel REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Bayan taron Shugabannin biyu a Berlin na kasar jamus, sun tsayar da shawara cim ma yarjejeniyar aiki da tsarin kasafin kudi tsakanin kasashen kungiyar Turai.

Shugaban Gwamnatin Jamus tace zasu ci gaba da tsara yarjejeniyar, tare da gaggauta zuba wasu kudade cikin asusun da za’a kaddamar cikin wannan shekara, saboda bada tallafi ga kasashen da suka shiga cikin wani hali.

Shugabanin kasashen Turai sun shiga duba yadda zasu tallafawa asusun ne, domin tunkarar matsalolin kudaden na Euro.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yace a tarihin Turai ba a taba samun irin wannan matsala ba, inda Shugabannin kasashen ke hana idanunsu barci domin warware matsalar.

Yanzu haka dai ayarin wasu kwararrun masana binciken harkan kudade suna kan hanyarsu zuwa Girka, makon gobe, domin gani da idanu, irin sauye-sauyen da aka samu bayan kama aikin Fira Minista Lucas Papademos.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.