Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta amince da karbar harajin hada-hada

Majalisar Kasar Faransa ta amince da wasu sabbin tsari na karban kudaden haraji, da ake ganin watakila wasu kasashen Turai su kwaikwayi haka.Shugaba Nicoklas Sarkozy ya bullo da wadannan matakai ne domin ceto kasar daga shiga mawuyacin hali da wasu kasashen dake amfani da kudaden Euro ke fuskanta.Karkashin sabon tsarin karban kudaden harajin da majalisar zartaswan Faransa ta bullo dasu, akwai karban haraji na kusan kashi daya cikin 100 daga kudaden sayen hannun jari daga masanaantu, masu babban Ofis a Faransa, da ma masanaantu dake da kudaden da suka kai Euro billion daya.Ma’aikatar kudin Faransa ta kiyasta cewa, idan har Majalisar kasar tayi na’am da tsarin , za’a fara aiwatar da shi, daga ranar daya ga watan 8 na wannan shekaran.na kididdige cewa Faransa zata rika samun kudaden da suka kai Euro biliyan 1, Da miliyan daya .Yanzu haka dai kasar Faransa da Jamus nata hankoron ganin kasashen Turai sun bullo da fasalin karban haraji na bai daya ne a kasashen su. 

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy REUTERS/Philippe Wojazer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.