Isa ga babban shafi
Faransa

Jam’iyyar Hollande ta samu rinjayen kujeru a majalisa

Jam’iyyar gurguzu ta samu rinjayen kujeru a zaben ‘Yan Majalisu da aka gudanar a ranar Lahadi, kuma wannan nasarar ce zata ba shugaba François Hollande damar aiwatar da alkawullan da ya dauka a lokacin yakin neman zaben shi.

Jadawalin sakamakon zaben 'Yan Majalisun Faransa
Jadawalin sakamakon zaben 'Yan Majalisun Faransa
Talla

Wannan ne karo na farko da Jam’iyyar gurguzu ta samu rinjaye kujeru a Majalisar Faransa bayan kwashe shekaru 10.

Jam’iyyar gurguzu da kwayenta sun samu nasarar lashe kujeru 314, inda kuma Jam’iyyar UMP ta tsohon shugaba Nicolas Sarkozy ta samu kujeru 191.

A lokacin yakin neman zaben shi, Shugaba Hollande ya sha alwashin fito da tsarin karin haraji ga masu hannu da shuni a Faransa, domin rage yawan kashe kudade a kasar.

Sakamakon zaben ‘Yan Majalisu dai ya nuna Jam’iyyar UMP ta sha kashi karo na biyu, bayan shan kashin Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasa.

A zaben ‘Yan Majalisu, ‘Yar takaran shugabancin kasar Faransa, kuma tsohuwar budurwar shugaban kasa, Francois Hollande, Segolene Royale, ta amsa shan kashi a zaben a lokacin da take jawabi ga magoya bayanta, amma Royal tace, duk da kayen da ta sha, zata ci gaba da taka rawa a siyasar Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.