Isa ga babban shafi
Ireland

An fara binciken cin zarafin yara a Ireland

A kasar Arewacin Ireland, a yau litinin an bude wani bincike kan zargin cin zarafin yara kanana da aka yi a ma’aikatu da kuma wuraren ibada, wanda zai kasance mai cike da dimbin tarihi.Ana sa ran daruruwan shaidu za su bayyana a gaban kwamitin binciken domin jin bahasin cin zarafin yara da aka yi a tsakanin shekarun alif dari tara da ashirin da biyu (1922) da kuma alif dari tara da casa’in da biyar (1995).Ana sa ran binciken da hukumomi suka kaddamar zaio duba cin zarafin da suka hada da jima’I, duka da kuma tozartar da yara da aka yi a gidajen reno da na marayu da kuma makarantu, cikin shekarun da bincike zai duba.Zuwa yanzu mutane 434 ne suka bayyana bukatar shiga don a dama da su a aikin binciken, kuma 61 daga cikin sun a kasar Australia ne, inda tawaggar bincike ta kai ziyara a a sheakarar bara, don neman shaidu.Ana sa ran a kalla mutane 300 za su bayar da bahasi, ko dai a su bayyana ko ta hanyar rubuto bayanan su, daga yanzu har zuwa wata Yunin shekara mai zuwa ta 2015.A watan Junairun shekarar 2016 ake sa ran tawaggar za ta mika rahoton ta, ga hukumomin arewacin Ireland. 

Fraiministan kasar Ireland Enda Kenny
Fraiministan kasar Ireland Enda Kenny REUTERS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.