Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya yi ikirarin samun nasarori a Faransa

Shugaba Francois Hollande zai cika shekaru biyu da darewa kan karagar shugabancin Faransa. Kuma a wata zantawa da wata mujalla, shugaban ya yi ikirarin samun gagarumar nasara wajen rage matsalolin da kasar ke fama da su.

François Hollande a wata ziyara da ya kai a Clermont-Ferrand
François Hollande a wata ziyara da ya kai a Clermont-Ferrand REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Francois Hollande ya tattaunawa ne da Jaridar Journal du Dimanche a jiya lahadi, kuma ya amsa cewa ya fuskanci manyan kalubale a shekaru biyu day a kwashe saman mulki.

Hollande mai ra’ayin gurguzu ya dandanta shekarun biyu da ya kwashe saman mulki a matsayin wata dama domin daura damara wajen tunkarar sauran matsalolin da kasar ke fama da su a cikin sauran shekaru uku da suka rage ya kammala mulkinsa.

Hollande yace idan aka yi dubi dangane da halin da Faransa ke a cikin shekaru biyu da suka gabata, ko shakka babu za a iya cewa akwai sauran aiki a gabansa, musamman abinda ya shafi rage gibi na tattalin arziki da kuma rashin ayyukan yi a tsakanin al’umma.

Shugaban yace tunkarar wadannan matsololi, shi ne abin da ke gaban gwamnatinsa, tare da yin alkawalin samar da ci gaba wajen farfado da tattalin arzikin kasar wanda ya tarar a cikin halin mafi kaskanci, da kuma yin sassauci ga ma’aikata da kamfanoni ta fannin makuddan kudaden haraji da ake karba daga gare su.

Sai dai har yanzu masana tsarin tattalin arziki na ganin cewa akwai babban aikin a gaban shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.