Isa ga babban shafi
Girka

Girka na fuskantar matsi daga Turai

Ministocin kudi daga kasashen Turai sun ci gaba da yin matsin lamba ga hukumomin kasar Girka, don su amince da yarjejeniya bashin da ake bin kasar. Amma Hukumomin birnin Athens sun kafe kan cewa ba za su aminta da bukatun kungiyr Turai ba.

Firaministan kasar  Girka Alexis Tsipras
Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras
Talla

Bangarorin biyu suna ci gaba da kokarin cim ma yarjejeniya, don kaucewa yuwuwar ficewar kasar Girka daga jerin kasashen da ke amfani da takardar kudin yuro.
Wannan na zuwa bayan taron da aka yi ranar litinin, inda aka tashi baram baran, inda dukkan bangarorin suka tsaya kan matsayinsu.

Cikin jawabin da ya yi a gaban majalisar dokokin kasar, Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras ya ce ba za su amince da kokarin ba ta musu suna ba.

Tsipras ya ce zai ci gaba da daukar matakan sauye sauyen da ya sa a gaba, wadanda suka yi hannun riga da tsare tsaren gwamnatin da ta shude.

Sai dai kasar ta Girka na ci gaba da zama saniyar ware, kuma tana ci gaba da hamayya tsakaninta da sauran kasashen da ke amfani da kudin na Yuro, karkashin jagorancin Jamus, da ke matsayin mai samar da kudaden tafiyar da gamayyar, da ba su son ganin hukumomin na Athens sun yi watsi na shirin na matse bakin aljihu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.