Isa ga babban shafi
Girka

Girka ta saki fatar karshe ta Bashin Turai akanta

Kasar Girka ta gabatar da bukatarta ta karshe ga kungiyar tarayyar Turai don neman tallafin rancen Kudi na tsawon Watanni 6, har zuwa lokacin da za ta kammala batun tsuke bakin Aljihu tsakaninta da kassahen da suka bata tallafin Kudi

Talla

A karon farko dai kasar ta Girka ta nemi Bashin takaitaccen lokaci ne, ya kuma zama makarkashiyar kulla huldayyar tattalin arziki tsakaninta da kassahe masu amfani da Kudin Euro ne, amma kuma daga baya ta kama neman karin wa’adin tsarin da ake bi, domin biyan kudaden, abinda ya nuna cewar dai har yanzu Girka na tuma tana faduwa ne a waje guda.

A karkashin manufofin gwamnatin kasar Girka da ta gabata dai, ya kamata gwamnatin kasar ta gabatar da gibin da ta samu na kasafin kudi da digo 3 ne a kowace shekara, kamin ta shiga biyan kudaden ruwa na Bashin da ta karba daga sauran kasashen Turai.

Amma wannan gwamnati mai kamawa ta ‘yan Syriza ta tsaya akan cewar gibin na digo 1 kacal ne za ta gabatar a kowace shekara.

Wannan ne ya sa a ranar farko ta tsayuwar sabuwar gwamnatin, ta fara nuna tirjiya ga bukatar hukumomin nan 3 da aka fi sani da suna “Troika” masu taimakawa kasar da Lamunin Kudi, da suka hada da Kungiyar tarayyar Turai, da Asusun bada lamunin kudi na Duniya da kuma babban Bankin kassahen Turai.

Kamin gudanar da zabe dai jagoran ‘yan adawa na wannan lokaci Alex Tsipras, yayi alwashin cewar za su kawar da kusan rabin Bashin da kasar ta Girka ke fama da shi na Euro Billiyan 320.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.