Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Kasashen Turai sun yi gargadi kan barkewar sabon rikici a Ukraine

Kasashen Turai sun bayyana bacin ransu, tare da bada gargadi bisa tabarbarewar yarjejeniyar tsagaita musayar wuta tsakanin ‘yan tawayen da ke goyan bayan Rasha da dakarun kasar Ukraine. Gargadin na zuwa ne, bayan barkewar fada a yankin Mariupol na kasar Ukrainem yayinda bangarorin biyu dake yaki, suke takaddama dangane janye manyan makaman yaki a gabashin kasar.Ganin yadda rikici ke cigaba da tsananta ne a garin Mariupol da kewaye, yasa hukumomi ke tunanin cewa, akwai yiwuwar ‘yan tawayen dake goyon bayan Rasha na shirin haifar da wani rikicin bayan harin da suka kai a Debaltserve, wanda ya bayyana warware yarjejeniyar tsagaita wuta da suka yi bayan makon daya gabata.Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar ta Ukraine, Andry Lysenko ya bayyana cewa a jiya Lahadi, an kai hari da tankokin yaki a Mariupol yayinda gwamnatin Ukraine ta zargi Rasha da aika tankokin yaki 20 da wasu motoci hade da mayan bindigogi zuwa ga yankin areawcin kasar. 

Dakarun kasar Ukraine cikin motar sulke a kusa da garin Artemivsk, a gabashin kasar
Dakarun kasar Ukraine cikin motar sulke a kusa da garin Artemivsk, a gabashin kasar Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.