Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

EU na neman hanyoyin warware rikicin kasar Ukraine

Kungiyar Tarrayar Turai na cigaba da tantance hanyoyin daya kamata abi, wajen warware rikicin Ukraine. Hakan dai na zuwa ne bayan da fadar Shugaban kasar Petro poroshenko ta sanar da wani zaman taro da kungiyar Turai ta shirya da hukumomin na Ukraine.Cikin wata tattauanawa ta wayar tarho da yayi da Shugaban kasar Ukraine Petro Porochenko, Shugaban tarrayar Turai Jean Claude Juncker ya cimma yarjejeniyar halartar wani taro, dangane da rikicin da ya dabaybaye kasar ta Ukraine .Za a dai gudanar da wanan taro ne ranar 27 ga watan Afrilu mai zuwa.Ukraine na daya daga cikin kasashen dake karkashin ikon tsohuwar Tarrayar Soviet, da kuma ke cigaba da samun goyan bayan kungiyar tarrayar Turai tun lokacin da Rasha ta ayyana goyan bayanta ga ‘yan aware dake fada da hukumomin kasar birnin Kiev.An dai soma gudanar da irin wanan taro ne tun bayan yarjejeniya da Ukraine ta cima da kungiyar ta EU, a cikin watan Yuni shekarar 2014 domin samun karin taimako daga wanan kungiya.Sai da Rasha na ganin wannan matakin a amtsayin tsokana a gareta .Ya zuwa yanzu EU ta tallafawa Ukrain da kudi kusan billiyan dubu daya da rabi na EURO, yayi da a daya wajen kuma hukumomin Rasha ke ciggaba da musanta cewa suna tallafawa yan tawaye masu neman balewa daga kasar ta Ukraine. 

Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko
Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko REUTERS/David Mdzinarishvili
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.